Kwastam ta kama kayayyakin da harajinsu ya haura milyan N74 a shiyyar Kaduna

Daga AISHA ASAS

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a shiyyar ‘Zone B’ mai hedikwata a Kaduna ƙarƙashin jagorancin Comptroller AB Hamisu, ta samu nasarar kama kayyakin da aka yi fasa-ƙwaurinsu wanda harajinsu ya haura Naira miliyan 74.

Bayanan hukumar sun nuna wannan kamen da hukumar ta yi ya faru ne cikin Fabrairun da ake ciki, ciki har da gano ɗaruruwan buhun shinkafar ƙetare da aka ɓoye a rumbunan ajiya daban-daban sassan shiyyar.

A cikin takardar sanarwa ga manema labarai da ta fito ta hannun Mai Magana da yawun hukumar na shiyyar Zone B, ASC1 MA Magaji, Hamisu ya lissafo kayayyakin da suka kama da suka haɗa da; shinkafar ƙetare buhu 635, motoci 13, manyan jarkoki ɗauke da fetur guda 232, katan 344 na spaghetti, da kuma tayar mota guda 183.

Sauran sun haɗa da manyan jarkoki na man girki guda 31 da matsakaita 12 da ƙanana 8, sai kuma buhun sukari 13, da madarar gari katan 149, da gwanjon sutura dila 6 da dai sauransu.

Jami’in ya ce baki ɗaya, harajin da ya kamata a samu a kan waɗannan kayayyaki da suka kama ya tashi N74,338,500.00.

A ƙarshe, Hamisu ya ce saurarn kayayyakin na nan an adana su a rassan hukumar daban-daban da ke shiyyar, kamar Neja, Kwara, Kogi, Kano, Kebbi Katsina da sauransu, waɗanda ba a samu jigilarsu zuwa babban ofishin shiyyar da ke Kaduna ba saboda wasu dalilai.