Kwastam ta kama kayayyakin fasa-ƙwauri na sama da milyan N66

Daga AISHA ASAS

A ci gaba da yaƙi da harkokin fasa-ƙwauri da take yi, Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a shiyya ta biyu (ZONE B) mai hedikwata a Kaduna, ta kama tarin haramtattun kayayyaki daga sassa daban-daban a shiyyar waɗanda a ƙiyasce kuɗinsu ya kai naira milyan N66,133,892.00.

Shugaban hukumar a shiyyar ‘Zone B’ Comptroller AB Hamisu psc(+) shi ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da suka gudanar a Larabar da ta gabata, tare da nuna kayayyakin da suka kama ga manema labaran.

Hamisu ya ce, kayayyakin da suka kama har da wuƙaƙe guda 180 a yankin Tsafe a jihar Zamfara, da motoci 13 da shinkafar ƙetare buhu 592 da manyan jarkokin man girki guda 227, jarkokin man fetur da dama, gwanjon sutura da dai sauransu.

Ya ce sun kama nau’o’in kayayyaki 51 tsakanin ranar 16 ga Fabrairu da 1 ga Maris, 2021.

Shiyyar Zone B na hukumar, ta ƙunshi jihohi guda 10 da suka haɗa da duka jihohi 7 na yankin Arewa ta yamma, da wasu ɓangarorin Arewa ta tsakiya haɗa da birnin tarayya, Abuja.

A cikin sanarwar manema labarai da Jami’in Hulaɗa da Jama’a na hukumar a Zone B, ASC1 MA Magaji ya fitar, ta nuns Comptroller Hamisu ya yi kira ga al’umma da a riƙa taimaka wa jami’ansu da muhimman bayanai da za su taimaka musu wajen ci gaba da yaƙi da harkokin fasa-ƙawauri a sassan ƙasa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*