Kwastam ta kama shinkafar ƙetare buhu 905 a cikin makonni biyu

Daga AISHA ASAS

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya ta ‘Zone B’ a Kaduna, ta baje kolin tarin kayayyakin da ta kama an yi fasa-ƙwaurinsu a tsakanin makonni biyu, a Maris.

A cewar Comptroller Al-Bashir Hamisu, sun samu nasarar kama waɗannan kayayyaki ne a wurare daban-daban a shiyyar.

Daga cikin kayayyakin da hukumar ta ce ta kama har da shinkafar ƙetare buhu 905 da man girki jarka 541 da dila 138 na gwanjon sutura da motoci guda 6 da dai sauransu.

Ga baki ɗaya, hukumar ta ce harajin da ya kamata a biya a kan waɗannan kayayyaki ya kai naira milyan N116.

Daga nan Comptroller Hamisu ya yi kira ga al’ummar ƙasa da su ci gaba da taimaka wa hukumar kwastam da muhimman bayanai domin daƙile harkokin fasa-ƙwauri.