Kwastom da sojoji sun fatattaki ‘yan fasa ƙwauri bayan kai wa jami’ansu hari a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kwastom ta Nijeriya, reshen ayyuka na tarayya, Zone A (FOU A), ta tabbatar da harin da ‘yan fasa-ƙwauri suka kai wa jami’anta da sojojin Nijeriya a yayin da suke gudanar da ayyukan yaƙi da fasa ƙwauri.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na sashin, SC Theophilus Duniya ya sanya wa hannu, a ranar Talata, 3 ga watan Yuni 2024, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni 2024 da misalin ƙarfe 3 na safe.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tawagar ‘yan sintiri ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi jami’an FOU A da wasu sojoji sun tare wani jirgin ruwa ɗauke da shinkafa da motoci ta ɓarauniyar hanya a bakin ruwa a garin Badagry na jihar Legas sun far wa tawagar, inda suka jikkata jami’an Kwastom da wani soja.

“Jami’an da ke aikin kare kansu sun nakasa shugaban ƙungiyar domin hana shi ƙara yi wa jami’an rauni kuma an kwashe su domin kula da lafiyarsu.

Da yake yaba wa jami’an bisa jarumtaka da sanin makamar aiki, Kwanturolan hukumar ta FOU A, Kola Oladeji, ya buƙaci iyaye da shugabannin al’umma da su dinga yi wa al’ummarsu nasiha daga aikata miyagun laifuka.

“Kwanturolan hukumar ta FOU A, Kola Oladeji, ya yaba wa jami’an soji da na kwastom bisa jajircewa da nuna ƙwarewa wajen tunkarar wani mummunan hari.”

Ya jaddada ƙudurin sashen na yaƙi da fasa ƙwauri. Ya kuma buƙaci iyaye da shuwagabannin al’umma da su jajirce wajen hana jama’arsu aikata miyagun ayyuka da ka iya jefa rayuwar su da sauran ‘yan ƙasa cikin haɗari.