Kwastom ta sayar da fetur ɗin da aka yi fasa ƙwaurin sa akan N630 kowacce lita

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kwastom, NCS ta yi gwanjon man fetur ɗin da jami’anta suka ƙwace bayan yin fasa ƙwaorin sa a Yola da ke Jihar Adamawa.

Kwantirola Janar, Bashir Adewale Adeniyi, wanda Mataimakinsa, Olaniyi Olagujun ya wakilce shi, ya bayyana hakan wa manema labarai a jihar inda ya ce sun sayar ne wa gidajen mai biyu akan N630 kowacce lita.

Ya ce, ƙwacewar da suka ya wani mataki da suka ɗauka a ƙoƙarinsu na cigaba da sanya ido kan ƙalubalen da ke fuskantar al’umma.

Adeniyi ya ce, ayyukan jami’ansu ya samu gagarumar nasara a ƙoƙarin su na yaƙi da fasa ƙwaurin fetur inda suka ƙwace manyan motocin fetur guda biyu masu nauyin ‘kegs’ 1,046 da kuma duro-duro 12 su ma na fetur.

Ya kuma yi gargaɗi ga masu ire-iren ayyukan, ya na mai cewa doka za ta yi aiki akan duk wanda aka kama da hannu acikin fasa ƙwaurin albarkatun ƙasa.

Kazalika, ya yi kira ga al’ummar da ke yankin kan iyaka da su bai wa hukumar haɗin-kai wajen daƙile aikace-aikacen da ke haifar da koma-baya wa ƙasa.