Kyakkyawar alaƙar aiki da gwamna ya sa na sauya sheƙa zuwa PDP, Inji Kakakin Majalisar Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Abubakar Yakubu Sulaiman ya bayyana cewar, shawarar sa ta komawa jam’iyyar sa ta asali, wato PDP ya biyo bayan kyakkyawar fahimtar da alaƙar aiki tsakanin sa da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.

“Ɗaya daga cikin dalilan daya sanya na koma jam’iyyar PDP ya biyo bayan fahimtar kyakkyawan shugabanci ne na gwamnan mu da kuma jajircewa da sadaukar da kansa wajen sakewa jihar fasali mai inganci. Don haka nasha alwashin yin aiki tare da shi domin amfanin ɗaukacin jama’ar jihar Bauchi”, a cewar Kakakin Majalisar.

Kakakin majalisar dokoki wanda ya yi waɗannan furutai na canjin sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa PDP a makon da ya gabata lokacin da yake yin buɗa-bakin azumi tare da Gwamna Bala Mohammed, haɗi da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga ƙananan hukumomin Ningi, Toro, Warji da Dass dake cikin jiha.

Ya ce, “Ina son yin amfani da wannan dama a yau domin bayar da sanarwa a hukumance wa mai girma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP batun komawa ta jam’iyyar PDP mai ci a jihar Bauchi.”

Kakakin Majalisar Dokokin ya kuma yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa kyakkyawar alaƙar aiki da yake da ita da majalisar dokoki ta jiha, wanda ya ce hakan ya yauƙaƙa samun nasarori da gwamnatin sa ta samu, husasan wajen samar wa jama’a ababen more rayuwa. 

Gwamna Bala Mohammed da yake karɓar shigowa kakakin majalisar cikin jam’iyyar PDP, ya ba shi tabbacin cewar, za a yi tafiya tare da shi dangane da dukkan lamura da suka jiɓanci jihar Bauchi, la’akari da tagomashi da ya yi wa jam’iyyar tasu.

Da yake yin la’akari da kyakkyawar dangantakar aiki dake wanzuwa a tsakanin majalisar dokoki da ɓangare gudanarwa na gwamnatin jiha, Gwamn Bala ya bayar da tabbacin cigaba da yin aiki tare domin bunƙasa wa da cigaban jihar Bauchi.

“Muna nuna godiyar mu wa Maɗaukakin Sarki Allah da ya tsawaita rayukanmu zuwa wannan wata mai tarin albarka na Sharu Ramadana muna cikin ƙoshin lafiya da kyakkyawan zamantake wa a ɗaukacin jihar Bauchi, kuma muna nuna godiyar mu gare ka a matsayin mashahurin mai ruwa da tsaki dangane da gudummawar ka data ƙarfafa kasancewa ta gwamnan jihar Bauchi a zaɓen gamagari da ya gabata.

“A yayin da muka amshi ragamar mulki, fannonin tattalin arziki na jihar Bauchi yana cikin matsanancin hali na baya tsiya gaba siyaki, don haka muke godiya ga Allah a yanzu lamura sun canja matuƙa gaya, musamman a ɓangarorin ilimi da kiwon lafiya, da wasu makamantan su, domin jurewa da ƙoƙarin mu sun samar da tagomasai na alfahari. Ina roƙon dukkan masu ruwa da tsaki dasu cigaba da bayar da gudummawa yadda kwalliya za ta biya kuɗin sabulu wa gwamnatin mu ta PDP a nan jihar Bauchi.”

Daga nan sai Gwamna Bala Mohammed ya bayar da umarnin kafa kwalejin Ilimi a cikin hurumin ƙaramar hukumar Dass ta jiha, tare da yin alƙawarin cigaba da gudanar da ayyukan alheri da zummar cika alƙawarorin sa na neman zaɓen gwamna da suka gabata a ɗaukacin faɗin jiha.