Kyakkyawar zamantakewa kaɗai za ta kawo zaman lafiya

A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu’amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra’ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama’a, daga ɓangarori daban-daban.

Babu shakka zaman lafiya da jama’a, tausayawa, tallafawa, da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama’a ke cikin ƙunci da rashin yarda da juna, saboda kurakuran da suke zargin wasu suna yi da gangan, don cimma wata manufa ta son ran su, ko danne haƙƙin wasu.

Rashin yarda, zargin juna, hassada, kishi, zalunci, babakere, da tauye haƙƙin raunana, halaye ne da aka saba gani a zamantakewa ta yau da kullum, inda wasu ke ƙoƙarin fifita kansu da tilasta buƙatun su kan na sauran mutane, a dalilin haka kuma sai a samu turjiya da nuna rashin yarda daga wani ɓangare.

Mummunar halayya irin ta hassada na ruguza imani da mutuncin mutum, saboda kasancewarta mugun ciwon da ke nuƙurƙusar mai yin ta a cikin zuciyarsa shi kaɗai.

Mun sha jin ƙorafe-ƙorafe daga mutanen da aka tauye wa haƙƙi ko aka zalunta, sakamakon son zuciyar da wani ya nuna musu, don kawai ya samu damar da zai yi abin da ya dace amma ya kasa, saboda zarmewa da son zuciya.

Akwai mutanen da za ka riƙa yi musu kallon manya ana girmama su saboda matsayin da suke da shi, ko arzikin da Allah ya ba su, har ma ka ji ana yi musu kirari, don kwaɗayin samun wata alfarma daga wajensu. Sai dai da a ce za ka samu jin abin da waɗanda ke ƙarƙashin sa ko iyalinsa suke faɗa, ba za ka so ka sake kallon sa da martaba ba. Saboda halinsa na rashin fitar da haƙƙin waɗanda suka yi masa ƙwadago da gumin su, sauke nauyin iyali da ‘yan uwa da ke kansa. Yana ganin idan ya cire wani abu daga arzikin sa to, zai rage masa jin daɗi, ko zai bayar a inda ba a san zafin su ba.

Yana yi wa mutane wahala su sadaukar da wani ɗan yanki na jin daɗin su, walwala ko damar da suke da ita don wani ya amfana. Sai ka ga ana ta fama da wani a cikin motar haya kan ya ɗan gyara zamansa domin kowa ya ji daɗin zama, amma mirsisi sai ya ƙi, saboda tunanin idan kowa ya zauna da kyau shi ba zai sake yadda yake so ba. Haka ma ko a gaban ubangiji wajen sauke farali, za ka ga wani ya yi babakere a waje ana roƙon sa ya gyara zama ko tsayuwar cikin sahu, amma yana ganin za a takura masa shi ba zai yarda ba.

A duk yayin da mutane suka fahimci wane yana da halin rowa, son kai da rashin sassauci a harkokin rayuwar to, yana zama abin ƙyama da yi wa kaffa kaffa. Kyautatawa da nuna halin kwarai suna sanya ƙaunar mutum a zuciyar abokan zamansa da sauran ‘yan uwa.

Sau da dama an sha samun asara mai yawa ta rai ko ta dukiya, da ɓacin rai mai tsanani, saboda wani ya kasa haƙuri a samu yadda ake so ko ya yi abin da ya kamata daga ɓangarensa, don yana ganin ba shi ne zai amfana ba, ko kuma idan ya yi haka zai takura.

Eh, ba an ce lallai mutum ya riƙa takurawa kansa don jin daɗin wasu ba ne, amma kyautatawa tana da amfani, kuma akwai alheri da ke bin bayan sadaukarwa ta tsakani da Allah. Ba kowanne lokaci ne yin abin da ya kamata ke zama takura ba, sauke nauyi ne. Kai ma wani lokaci za ka nemi wani abu daga wajen wani, wanda ka ke ganin ya kamata ya yi maka, idan bai yi ba kai ma ba za ka ji daɗi ba.

Mutane masu son zuciya ba sa taɓa samun wadata da gamsuwa da rayuwar su, ko da kuwa sun samu damar yin duk abin da suke so, saboda ko da yaushe tunanin su ba ya wuce jin daɗin kansu ta hanyar ƙuntatawa wasu.

Don haka kirana ga mai karatu shi ne a guji fifita son rai, domin an ce son zuciya ɓacin zuciya!

Wasiƙa daga AHMADU ISA, 09070905293.