Kyawun alƙawari: Buhari ya yi wa Tawagar Super Eagles a gasar Tunisiya 1994 kyautar gidaje

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a ba da kyautar gida mai ciki uku-uku ga kowane ɗan wasan Super Eagle na tawagar da ta ciyo wa Nijeriya Kofin Afirka a gasar da aka gudanar a ƙasar Tunisiya a 1994.

Wannan kyauta na mazaunin cika alƙawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa ‘yan wasan ne a wancan lokaci sakamakon nasarar lashe gasar da suka samu.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta nuna gwamnati ta cika wannan alƙawari ne bayan da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya aika wa Shugaban Ƙasa da takarda kan batun gidajen. Tare da cewa kafin wannan lokaci, shida daga cikin ‘yan wasan da wasu ma’aikata su uku sun rigaya sun samu nasu gidajen.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, ‘yan wasan da lamarin ya shafa sun haɗa da: Peter Rufai, Alloy Agu, Ike Shorounmu, Uche Okechukwu, Samson Siasia, Efan Ekoku, Sunday Oliseh, Benedict Iroha, Isaac Semitoje, Mutiu Adepoju, Emmanuel Amunike, Victor Ikpeba, Austin Eguavoen da kuma marigayi  Wilfred Agbonavbare.

Sauran su ne: marigayi Uche Okafor, marigayi Thompson Oliha, marigayi Stephen Keshi, Christian Chukwu, Dr Akin Amao, Stephen Edema, Col. A Asielue sai kuma B. Aromasodun.