Kyawun alƙawari cikawa

Daga IBRAHIM YAYA

A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma hukumomi da masana a fannin yaƙi da sauyin yanayi na yin gargaɗi game da yadda yunwa da fari da sauran bala’u daga indallahi za su iya addabar sassan duniya.

Kuma ana iya ganin haka a wasu sassa na duniya dake fama da matsaloli na ambaliyar ruwa ko mahaukaciyar guguwa dake tafe da ruwan sama da ma fari a wasu sassa na nahiyar Afirka da makamantansu.

Masana dai sun sha yin gargaɗi tun ma kafin ɓullar annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yaƙin duniya na biyu, saboda wasu dalilai.

Na baya-bayan shi ne, kiran da hukumomin agaji da dama suka yi na gaggauta samar da ƙarin kuɗaɗe da shugabanci na-gari, don tinkarar gagarumar matsalar ayyukan jin kai dake fuskantar miliyoyin mutanen dake zaune a shiyyar gabashin Afrika sanadiyyar matsanancin fari, har ma aka yi kashedin cewa, muddin aka yi jinkiri to, babu makawa rayukan jama’a da dama na iya salwanta.

Haka ma ƙwararru daga nahiyar Afirka sun buƙaci ƙasashen da suka ci gaba, da su cika alƙawuran da suka dauka, na samar da isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan daƙile sauyin yanayi, yayin taron COP27 da zai gudana a birnin Sharm El-Sheikh na ƙasar Masar.

A cewarsu ƙasashen da suka ci gaba ne ke fitar da kaso mafi yawa na iskar Carbon mai dumama yanayin duniyarmu, don haka ya dace su samar da kuɗaɗen rage tasirin sauyin yanayi ga ƙasashe masu tasowa, waɗanda ke ɗanɗana kuɗa sakamakon rashin karfinsu na tunkarar wannan ƙalubale.

Domin idan babu kira to me zai ci gawayi.

Ko da a watannin da suka gabata ma, ƙasashen Afika da dama sun sha fama da wasu daga cikin munanan tasirin sauyin yanayi, ciki har da ambaliyar ruwa a Najeriya, da fari a yankin ƙahon Afirka.

Saboda haka, nahiyar Afirka na fatan sauran sassan duniya za su fahimci mummunan tasirin da nahiyar ke fama da shi daga sauyin yanayi.

Idan ba a manta ba ƙasashe masu wadata sun yi alƙawarin baiwa nahiyar Afirka gudummawar dalar Amurka biliyan 100 a duk shekara, domin gudanar da ayyukan daƙile tasirin sauyin yanayi, amma har yanzu shiru ka ke ji, wai malam ya ci shirwa.

Idan har duniya na fatan magance matsalar tasirin sauyin yanayi, ya dace taron na wannan karo, ya duba alƙawuran da aka yi yayin taron COP26 na birnin Glasgow, ta yadda za a fitar da kyakkyawan tsarin aiwatarwa, wanda kowa zai amince da shi. Domin kyan alƙawarin aka ce cikawa.

Kuma wannan shi ne dattaku
Matsalar sauyin yanayi, na ƙara sanya tarin jama’a ƙauracewa muhallansu lamarin dake sanadiyyar fadawar ƙarin mutane cikin yanayin tsananin buƙata.

Wannan ne ma, ya sa masu fashin baki ke cewa, yanzu ne lokacin da ya dace na ɗaukar matakai, domin kaucewa faɗawar miliyoyin al’ummomi, musamman dake shiyyar gabashin Afrika cikin garari.

Aka ce da zafi-zafi kan bugi ƙarfe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *