Labaran Maku ya yi alƙawarin cigaba daga inda Marigayi Akwashiki ya tsaya

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Tsohon ministan labarai da al’adu Labaran Maku yace zai cigaba da gudanar da ayyukan cigaba da Marigayi Akwashiki ya tsaya idan ya gaje shi a kujerar sanatan.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara tare da tawagar yaƙin neman zaɓen sa gidan su Marigayi Akwashiki da ke Angba-Iggah a ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon ta jihar Nasarawa.

Mista Akwashiki Awalaro mahaifin marigayi sanatan ya tarbi tawagar. A cewar wakilinmu mai faɗa aji na gidan Akwashiki ɗin ya bayar da goyon bayansa ga tsohon ministan a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin ɗan sa.

Da ya amshi goyon bayan Maku, wanda ya taɓa zama mataimakin gwamnan jihar ya yi alƙawarin tabbatar da gadowar marigayi sanatan ta hanyar ayyuka masu inganci.

Daga cikin abubuwan da ya yi alƙawari akwai,
kammala dukkan ayyukan da marigayi sanatan ya fara da riƙe tawagar Akwashiki ciki har da mataimakansa da ma’aikatansa idan ya yi nasara a zaɓe da kafa gidauniya da sunan marigayi ɗan majalisar don horar da shugabanni da tallafawa marasa ƙarfi a faɗin mazabar Nasarawa ta Arewar.

Maku ya kuma jaddada aniyarsa ta samar da ayyukan yi da ƙarfafa matasa da mata da kuma neman ƙarin ayyukan gwamnatin tarayya domin inganta rayuwar al’umma a Nasarawa ta Arewa.

Sanata Akwashiki shi ne mafi ƙwarewa a cikin sanatocin da jihar Nasarawa ta taɓa samu saboda nasarorinsa da ci gaban da ya kawo. Zan bai wa al’umma wakilci mai inganci da shugabanci mai ma’ana,” in ji Maku.

Da yake jawabi a baya Awalaro ya ce dalilin da ya sa suka goyi bayan Maku shi ne domin girmama umarnin marigayi ɗansa: “Dana, Marigayi Sanata Godiya Akwashiki, ya gaya mun da iyali cewa idan ya rasu mu goyi bayan Mista Labaran Maku ya maye gurbinsa a Majalisar Dattawa.”

Ya ƙara da cewa Akwashiki da yake raye yakan faɗa musu yadda Maku ya taimaka masa sosai a lokacin yaƙin neman zaɓen sa ciki har da ƙin karɓar kyautar kuɗi daga gare shi inda yace a maimakon haka a yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da ayyuka a al’ummomin Nasarawa ta Arewa.

“Hanya ɗaya tilo da za mu sakawa Maku ita ce dukan iyali su goyi bayansa su zabe shi,” in ji Awalaro.

Wakilin namu a jihar ya kuma ruwaito cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) dai ta sanya ranar 20 ga yunin nan domin gudanar da zaɓen fidda gwanin kujerar Nasarawa ta Arewar bayan mutuwar shi tsohon sanatan wato Godiya Akwashiki.

By ukarofi

Leave a Reply