Labari da ɗuminsa: Gwamnatin Neja ta haramta acaɓa

A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a jihar Neja, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Abubakar Sani Bello ta kafa dokar haramta acaɓa a faɗin Minna, babban birnin jihar.

A cewar Gwamnatin wannan doka za ta soma aiki ne daga ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, 2021.

Sai dai sabuwar dokar ta sahale wa masu babura na kansu da su riƙa zirga-zirga daga ƙarfe 6 na safe zuwa 9 na dare.

Jihar Neja na daga cikin jihohin da ke matsanancin fama da matsalar ‘yan bindiga, domin ko a baya-bayan nan sai da wasu ‘yan fashin daji suka sace ɗaliban Islamiyya su kusan 200 a Tegina wanda har yanzu ba a kai ga kuɓutar da su ba.