Labari da zafi-zafinsa: Buhari ya kira taron gaggawa kan sha’anin tsaron ƙasa

Yanzu haka Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na kan ganawa da shugabannin tsaro a wani taron gaggawa da ya kira kan sha’anin tsaron ƙasa.

Taron na gudana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ƙasa MuhammaduMBuhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, Shugaban Tsaro, General Lucky Irabor; Shugaban Sojijin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu, Shugaban Sojojin Sama, Air Marshal Isiaka Amoo da kuma sabon Shugaban Sojoji, Major General Farouk Yahaya.

Sauran su ne, Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba; Shugaban Cibiyar Tattara Bayanan Sirri (NIA), Ahmed Rufa’i; Darakta Janar na DSS, Yusuf Bichi, da sauran ƙusoshin gwamnati.

…a tarbe mu anjima don ƙarin bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *