Lafiya lau za a yi zaɓukan 2023 ba tare da rikici ba – Monguno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a gudanar da zaɓen 2023 ba tare da rikici ba.

Monguno ya bada wannan tabbacin ne yayin ganawarsa da Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da kuma shugabannin hukumomin tsaro a ƙasar.

Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da duk wani nau’i na ɓata-gari, labaran ƙarya da fargaba kan yadda za a gudanar da babban zaɓen 2023, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Monguno ya ce taron na da nufin duba wasu batutuwan da suka mamaye fagen siyasa da tattalin arzikin ƙasar a cikin makonni biyun da suka gabata, wanda ya haifar da fargaba, tashin hankali, tsoro da rashin tabbas dangane da babban zaɓen ƙasar.

“Dukkanmu mu na sane da halin da ƙasar nan ke ciki. Akwai buƙatar in tabbatar wa ‘yan ƙasar nan cewa duk wani tsoro, ko tashin hankalin da muke da shi, zan so in kawar da irin wannan tunanin.

“Zaɓen 2023 zai gudana ne a cikin yanayi mai kyau ba tare da tashin hankali ba. Hukumomin tsaro sun yi abubuwa da yawa a cikin watanni biyun da suka gabata don tsara abubuwa.”

Monguno ya ce hukumomin tsaro na da tabbacin matakan da suka ɗauka.