Lafiyar Ma’aurata: Ciwon Sanyi

Daga BILKISU YUSUF ALI

Gabatarwa:
Wannan sabon shafi mai suna Lafiyar Ma’aurata shafi ne wanda za mu riƙa gabatar mu ku da shi, domin tattaunawa kan al’amuran da su ka shafi sha’anin lafiyar ma’aurata da dangoginta, inda Anti Bilkisu Yusuf Ali, wacce malamar jami’a ce kuma marubuciya mai nazari kan harkokin zamantakewa za ta riƙa kawo mu ku mafita kan matsalolin rashin lafiya da ke addabar zamantakewar aure. Ku na da dama ta aiko da tambaoyinku kai-tsaye a adireshi ko lambar wayar da ke can ƙasa, domin warware mu ku ta hanyar ba ku amsoshi.

Tambaya: Anti Bilkisu barka da yamma Ina tambaya ne kan maganin sanyi na jima ina fama da matsalar rashin ni’ima da ƙarancin sha’awa sai aka ce ciwon sanyi ne shi ne nike son bayani kan ciwon sanyi da hanyoyin magance shi.

Ciwon sanyi:
Mutane da dama sukan shiga ruɗani ganin yadda ake yawan yin magana akan ciwon sanyi wasu na ganin kowacce cuta sanyi ne silarta inda wasu ke ganin kamar shaci faɗi ne babu wani abu mai suna sanyi. Zance ma fi inganci daga masana suna cewa ma fi yawancin al’umma suna ɗauke da ciwon sanyi amma tunda ba sa jin kowanne nau’in ciwo ba su san suna ɗauke da wannan nau’in ciwon ba. Ciwon sanyi ma’aurata kan ɗauka yayin kusantar juna haka ana ɗaukarsa a banɗaki da mai cutar ya shiga ya yi amfani da shi. Ciwon sanyi ciwo ne mai wuyar sha’ani saboda yadda yake yaɗuwa ya jima a jiki ba a sani ba. Mata sun fi yawan kamuwa da ciwon sanyi saboda yanayin halittarsu da yadda suke amfani da banɗakuna musamman na zama sannan za ka sami namiji yana da mace biyu ko ma fiye kuma in har da guda mai wannan ciwo na sanyi dukansu suna iya samu.

Alamomin ciwon sanyi:
Ciwon sanyi yana da alamomi da dama amma wanda masana suka fi ambata sune:-

  • Ƙaiƙayin gaba ko na jiki musamman idan aka zuba ruwa a jiki
  • Ƙaiƙayin gaba
  • Rashin Sha’awa
  • Ɗaukewar ni’ima
  • Zubar farin ruwa
  • Jin zafi yayin kusantar juna (ma’aurata)
  • Al’ada ta riƙa yin wasa
  • Rashin ƙarfin gaba gun namiji

Ciwon sanyi yana da maguguna da dama wanda za mu faɗe su anan kuma in sha Allah in an gwada ana dacewa. Yana da kyau amare kafin a fara ba su magunguna don ni’ima ko sha’awa a fara ba su maganin sanyi haka ke ma uwargida ki ke haɗawa da maganin sanyi saboda da dama akan kasa gane kyawun magani komai kyansa in an sha in har jiki da akwai ciwon sanyi.

Maganin sanyi na ɗaya:
Ki sami kaza ƙarama ba babba ba a yanka a ɗebe kayan cikin a wuyanta sai a wamke sosai. A samu ƙwayoyin tafarnuwa cikin tafin hannu amma hannu madaidaici a samu garin kanumfari cikin ƙaramin cokali a samu garin turmeric /Kurkum shi kuma rabin ƙaramin cokali a samu garin yansus cikin naramin cokali a zuba a cikin kazar nan da aka kwashe kayan cikinta sai a ɗinke. Sai a ɗora a wuta tare da dukkan kayan miya da duk abin da ake saka wa yayin farfesu sai dai kada a cika ruwa saboda ana son wannan maganin da aka zuba a cikin kazar ya haɗu. In ta dahu ta yi sanyi sai a cinye. In sha Allah in dai an yi wannan kowanne irin nau’in sanyi ne za a samu warakarsa da yardar Allah.

Maganin sanyi na biyu:
Ana dafa lalle da kanumfari a sa miski kaɗan da bagaruwar mata ki ke zama a ciki in ya huce ko da minti biyar zuwa goma ne sannan kuma kina iya kama ruwa da shi ko sau biyu ne a rana. Wannan yana da matuƙar muhimmanci wajen tsaftace gaban mace da kashe kwayoyin cuta. Amma a kula yayin haɗawar kada a yi amfani da mahaɗi marar kyau ko kuma a zauta awon ko a ƙaranta shi.
In sha Allah mako na gaba za a ji mu da wani na’in maganin sanyin.

Amma ki sani babban maganin sanyi irin wanda ake ɗauka shi ne tsafta ta jiki da kuma ta banɗaki da ‘pant’ ɗin da ki ke amfani da shi tare da tsaftarsa.

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko ta whatsApp 08054137080 ko ya duba shafin Facebook ɗina mai suna Bilkisu Yusuf Ali, ko ta imrel: [email protected] ko kuma Ilham Special Care And Treatment.