Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Daga AISHA ASAS

Bisade Ologunde, wanda duniya ta fi sani da suna Lagbaja, mawaƙin Nijeriya ne da Allah Ya wadata da baiwar waƙa. Mawaƙi ne da ke da hikimar rera waƙa da mabambantan kiɗa, domin ya ƙware ƙwarai wurin sarrafa waƙz’a mai amfani da kifan zamani da kuma na al’adarsu, wato Yarbanci.

Kamar yadda muka sani, kaso mai rinjaye na masu harkar nishaɗantarwa, kama daga waqa, kixa zuwa wasan kwaikwayo ko wasannin barkwanci zuwa na wasan motsa jiki, za ka tarar da a layin farko ko na biyu na burukansu akwai shahara, duniya ta san da su, duk inda suka shiga a gane su da fuskokinsu, masoya su dinga turuwan son ganin su.

Da yawa wannan matakin ne za su taka su san cewa, lallai sun zama wata tsiya a harkar nishaɗantarwa, don haka ne suke zage damtse wurin ganin sun aikata ababen da za su iya kai su ga irin wannan matsayi da ya zama burinsu tun a daren farko a duniyar nishaɗantarwa.

Idan mun yi duba da irin ababen da wasu ke yi a kafafen sada zumunta na wannan lokaci na daga ababen da ke zubar masu da mutunci ko janyo cece-kuce, musamman a wurin mata, yayin da ka yi dogon bincike dakyar ba ka tarar da neman suna a ciki ba.

Wasu mutane za su aikata abinda ma zai janyo musu zagi, amma kaga suna murna da abin, sakamakon haƙarsu da ta cimma ruwa, wato mutane da dama sun san da zamansu ta sanadiyar abin magana da suka yi.

Haka ma in mun leqa masana’antun shirya fina-finai, akan samu wani kaso mai ɗan nauyi musamman a cikin mata da ke shiga masa’antar ba don samun na rufa wa kai asiri ba, sai don fatan a sa su a fim su yi suna, duniya ta san da zaman su.

Da wannan ne zai kasance abin mamaki idan aka samu wani a duniyar yana ƙoƙarin ganin ba a san da zamansa ba, ko in ce an san shi, amma ba a san fuskarsa ba. wasu da yawa sukan ga hakan a matsayin rashin sanin abinda ya kamata, domin sanin fuskar jarumi ko mawaqi na xaya daga cikin romon zama a matsayin.
Bisade Ologunde, ya kasance mawaqin da ya samu suna da shahara, kuma yake da ɗimbin masoya da ke sauraron waƙoƙinsa a ciki da wajen Ƙasar Nijeriya, sai dai ko kaɗan ba shi a layin mawaƙan da suke burin a san da su, ko a iya gane su ta fuska.

Da yawa daga cikin waxanda suka samu shuhura sukan yi ƙorafin rashin damar walwala tsakanin al’umma sakamakon yadda idon mutane ke kansu, sukan bayyana cewa, sau dayawa sukan yi sha’awar yin wasu abubuwa, kamar fita ƙofar gida ka zauna gindin bishiya, ka sha iska, ko zuwa kasuwa da makamantansu, amma shaharar da suke da ita ta hana su, sai dai ba kasafai ka ke jin suna ayyana wannan a matsayin nadamarsu ko idan an ba su damar canza wani abu a shaharar za su iya canza shi ba. Da wannan za mu iya cewa, abu ne da ke takura masu, amma yana cikin ababen da suka fi so a cigaban da suka samu.

Ko kaɗan a ɓangaren mawaƙi Lagbaja ba haka ta ke ba, domin da ya ɗaura aniyyar shiga yaƙin neman gwaninta a ɓangaren waƙe, sai ya adana fuskarsa, ya yi tafiyar da iya muryarsa kawai, kuma har ya yi nasarar samun shaharar bai sa ya canza ra’ayinsa na bayyana fuskarsa ga ɗimbin masoyan waƙoƙinsa da suka kwaɗaitu da son ganin fuskarsa ba. Wannan dalilin ne ya sa ake masa kirari da ‘Faceless’, ko ‘Anonymous’, wato marar fuska, ko kuma wanda ba a sani ba.

Da wannan ya jima yana jan ruwa a duniyar ma’abuta sauraron waƙoƙinsa, fuskarsa ta zama babban buri da kowa ke fatan gani ko kuma zama silar bayyana ta ga al’umma. Dalilin kenan da ya sa ake saka shi layin farko a jadawalin ababen da ke fatan son gani game da wasu masu muhimmanci.

An haifi mawaƙi Lagbaja a Jihar Iko, a ranar 1 ga watan Junairu, shakarar 1960. Asalinsa tsatson Jihar Kwara ne, a wata ƙaramar hukumar da ake kira Oyun.

Rayuwar mawaƙin da ta shiga duniya gajeruwa ce, kamar yadda sanin sa yake, sai dai an samu labarin mahaifinsa sunansa Deacon D.A Olugunde, kuma ya mutu a shekarar 2012. Kuma ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Jihar Kwara a matsayin ma’aikacin tsaro, sannan babban limamin Coci ne.

Mawaqi Lagbaja ya samu karatu mai zufi daidai gwargwado, duk da cewa, bai bayyana makaratun da ya yi ba, sai dai an samu labarin ya yi karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo, wanda hakan ya tabbar da ya ilimintu. Ababe da dama game da rayuwar mawaƙin sun kasance sirrin da ya ɓoye, a ƙoƙarinsana ganin fuskarsa ba ta bayyana ba.

Lagbaja ya fara harkar waƙa a sheka ta 1990, shekara ɗaya bayan haka, ya ƙaddamar da qungiyar makaɗan sa, wanda suka zama masu wasa a ‘Sea Garden’ a ko da yaushe.

Yanzu haka dai mawaqi Lagbaja na da aure da ‘ya’ya, sai dai har yanzu bai tava bayyana hoton matarsa ba, wataƙila hakan bai rasa nasaba da ƙoƙarin ƙara ba wa kamaninsa kariya daga al’umma. Duk da haka, an ruwaito cewa, ɗaya daga cikin ɗiyan mawaƙin ta yi suna a matsayin ɗiyar mawaƙin mai suna Moyosade, sai dai hakan bai sa aka samu tabbacin fuskar mawaƙin. Duk da cewa, a ranar aurenta da aka yi a shekarar 2013 ya halarci bikin ba tare da rufe fuska ba, hakan ya sa wasu ke iƙirarin sun samu hotonsa, duk da cewa wata majiya ta ce, an haramta ɗaukar hoto ga kowa bayan mai hoton da ma’auratan suka ɗauka.

A wata majiya, dalilin da ya sa mawaqi Lagbaja yake rufe fuskarsa na da alaƙa da gidan da ya fito, kasancewarsa ya fito daga gidan malaman Coci, wanda wasu ke cewa, shi karan kasan na ɗaya daga cikin waɗanda ke waƙoƙin yabo a Cocin da iyayenshi ke zuwa. Baya ga wannan wannan an samu wasu batutuwa da dama kan dalilan da suka sanya mawaƙin rufe fuskanashi, don haka tsayawa a matsaya ɗaya, ko yarda da batu guda zai yi wuya, sai dai abinda na sani, kowa kaga ya yi wani abu yana da dalilin da ya sa ya yi shi, koda kai hakan bai yi daidai da naka ra’ayi ba.

Koma me ye dalilin nasa, hakan ya zame masa alkhairi, domin ya ƙara masa shahara a tsakanin mutane, kasancewar wasu sun fi sha’awar sanin fuskarsa ma fiye da waƙoƙin da yake yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *