Laifukan zaɓe da yadda za a ƙaurace musu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau Asabar miliyoyin ’yan Nijeriya masu katin zaɓe za su fita rumufunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’ar zaɓen shugaban da zai gaji Muhammad Buhari.

Baya ga shugaban ƙasa, ’yan ƙasar za su zaɓi ’yan Majalisar Wakilia 360 da kuma sanatoci 109 a zaɓen yau ranar Asabar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro sun bayyana shirinsu na tunkarar babban zaɓe na yau.

Za a gudanar da zaɓukan ne a mazaɓu 1,491 da ke ƙananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zaɓe 176, 846 a kasar mai jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Alƙaluman da INEC ta fitar sun nuna kasarin ’yan ƙasar da za su yi alƙalanci a zaɓen matasa ne, masu shekara 18 zuwa 35.

Yayin da ’yan Nijeriya ke shirin fara zaɓen shugabanninsu na gaba yana da kyau masu kaɗa ƙuri’a su fahimci laifukan zaɓe da yadda za su ƙauce musu a lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.

Ga jerin wasu muhimman laifuka da dokar zaɓen Nijeriya ta 31 ga watan Disambar 2018 ta tanada;

  1. Laifukan da suka shafi takardar ƙuri’a da akwatin zaɓe:

Mallakar takardun ƙuri’a ba bisa amincewar dokar zaɓe ba da gurza takardar ƙuri’a ba bisa ƙa’ida ba da kuma haɗawa da shigo da akwatunan zaɓe cikin Nijeriya ba da amincewar dokar ƙasa ba.

Hukunci: Duk wanda aka samu da aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 50,000,000.00 ko ɗauri a kurkuku da bai gaza na shekara 10 ba ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin.

  1. Amfani da katunan zaɓe ba bisa ƙa’ida ba:

Miƙa wa wani katin zaɓenka da niyyar ya kaɗa ƙuri’a da shi yayin wani zaɓe ko kasancewa da katin zaɓe fiye da ɗaya, laifi ne a ƙarƙashin wannan doka ta zaɓe.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 1,000,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda ba zai gaza na wata 12 ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Jigilar mutane a lokutan zaɓe:

Ɗaukar masu zaɓe a mota zuwa wata rumfar zaɓe a cikin motar gwamanti ko kwale-kwale na gwamnati laifi ne ƙarƙashin dokar zaɓen ta Nijeriya.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda bai gaza na wata shida ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Yin zaɓe ga waɗanda ba su cancanci yinsa ba:

Duk wanda aka samu yana kaɗa ƙuri’a ko ƙoƙarin kaɗa ta yayin wani zaɓe da hukumar zaɗe ta shirya duk da bai cancanci yin zaɓen ba ko kuma jan hankalin wani ya yi zaɓe alhalin bai cancanci yin zaɓe ba laifi ne ƙarƙashin wannan dokar.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda bai gaza na wata 12 ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Wasa da aiki ko sanarwa ko wallafa sakamakon zaɓe na bogi:

Duk jami’in zaɓen da bai hallara a rumfar zaɓen da aka tura shi ya gudanar da zaɓe ba a kan lokaci, ko wanda ya ƙi yin aikinsa kamar yadda doka ta tanadar ko kuma wanda ya sanar ko ya wallafa sakamakon zaɓe na bogi, dukkansu sun aikata laifukan zaɓe.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda bai gaza na wata 12 ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare. Akwai kuma tanadin ɗaurin wata 36 ga wanda ya aikata laifi na biyu a ƙarƙashin wannan sashen.

  1. Sanarwa da wallafa sakamakon zaɓe na bogi:

Dukkan jami’an zaɓen da suka sanar ko wallafa wani sakamakon zaɓe na bogi sun aikata laifukan zaɓe.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin ɗauri a kurkuku na tawon shekara uku kuma babu zaɓin a yi masa tara.

  1. Bayar da cin hanci da kitsa aikata laifuka:

A ƙarƙashin wannan tanadin, akwai aikata laifukan cin hanci da rashawa da kuma karɓar kyaututtuka domin kaɗa wa wani ɗan takara ƙuri’ ko ma yin fashin kaɗa ƙuri’a.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tarar da ba ta wuce Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku wanda bai gaza na wata 12 ba, ko ma a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Tabbatar da yin zaɓe cikin yanayi na sirri:

Wasu laifukan sun haɗa da ƙin samar da yanayin sirranta kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe da hana wasu mutane damar kaɗa ƙuri’a.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 100,000.00 ko ɗauri a kurkuku na wata shida, ko a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Kaɗa ƙuri’a da sanar da bayanan ƙarya:

Duk wanda ya aikata wani laifi na kaɗa ƙuri’a ba yadda doka ta tanada ba, da wallafa wata sanarwar ƙarya cewa wani ɗan takara ya janye daga shiga zaɓe ko wata sanarwar da ta ɓata sunan wani ɗan takara, ya aikata laifin zaɓe.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 100,000.00 ko ɗauri a kurkuku na wata shida, ko a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Yin zaɓe ba tare da yin rajista ba:

Dukkan wanda ya yi zaɓe ba tare da an yi masa rajista ba ta hanyar amfani da wani katin zaɓe mallakin wani mutumin na daban, shi ma ya aikata laifin zaɓe.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 100,000.00 ko ɗauri a kurkuku na wata shida, ko a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

  1. Tayar da hargitsi yayin gudanar da zaɓe:
    Shi ma wanda ya tayar da hargitsi yayin da ake gudanar da zaɓe domin tunzura wasu mutanen na daban su tayar da hankulan al’umma, shi ma ya aikata ɗaya daga cikin laifukan zaɓe.

Hukunci: Duk wanda ya aikata wannan laifin zai fuskanci hukuncin tara ta Naira 500,000.00 ko ɗauri a kurkuku na wata 12, ko a ɗora masa tarar da ɗaurin tare.

Akwai kuma wani tanadin da ke cewa za a iya ɗaure mutum har tsawon wata 24 idan aka kama shi yana aikata laifin sace kayan zaɓe ko lalata su.