Muƙaddashin babban hafsan sojojin ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya isa jihar Sakkwato domin ziyarar aiki ta farko zuwa yankin da rundunar sojin Nijeriya ta takwas ke da alhakin kula da shi.
Rahotanni daga News Point Nijeriya sun nuna cewa a wannan ziyara, Oluyede zai gana da Sarkin Musulmi, Sultan na Sakkwato, tare da wasu masu ruwa da tsaki a cikin yankin da rundunar ta takwas ke aiki. Ziyarar ta kuma bai wa Oluyede damar jawabi ga dakarun rundunar Operation Fasan Yamma da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.
Ziyarar muƙaddashin babban hafsan sojin Nijeriya ta zo ne bayan kwanaki uku da hedikwatar tsaro ta tabbatar da bayyanar wata sabon ƙungiyar ta’addanci da ake kira ‘Lakurawa’ a jihohin Sakkwato da Kebbi. An bayyana cewa ƙananan hukumomi guda biyar a jihar Sakkwato na fama da barazanar wannan sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa.
Babban jami’in ayyukan tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa ƙungiyar Lakurawa na ƙara ta’azzara rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, amma dakarun Nijeriya na iya ƙoƙarin shawo kan su. Ya ce, “Dakarun mu suna fuskantar sabuwar ƙungiyar ta’adda a Arewa maso Yamma da ake kira Lakurawa, waɗanda ke da alaƙa da ‘yan ta’adda daga Sahel, musamman daga ƙasashen Mali da Jamhuriyar Nijar.”
Buba ya ƙara da cewa wannan sabuwar ƙungiyar ta ɓullo ne daga Mali da Nijar bayan juyin mulkin da ya kawo cikas ga haɗin gwiwar soji tsakanin Nijeriya da Nijar. Haka kuma, sojin Najeriya sun ayyana wasu ‘yan ta’adda guda tara da ake nema ruwa a jallo saboda rawar da suke takawa a ƙalubalen tsaro da ke damun ƙasar.