Lakurawa na da hannu a harin bom ɗin Zamfara, inji ‘yan sanda

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta zargi sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna Lakurawa da hannu a fashe-fashen boma-bomai da suka auku a hanyoyin ƙauyuka biyu a yankin Ɗansadau, ƙaramar hukumar Maru.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammad Shehu Dalijan, ya bayyana hakan yayin wata hira ta wayar tarho da wakilinmu.

A ranar Laraba, News Point Nigeria ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun dasa bama-bamai a hanyar dake tsakanin Ɗansadau da Gusau, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar matafiya.

Shaidun gani-da-ido sun bayyana yadda bam ɗin ya hallaka mutane shida tare da jikkata wasu takwas bayan wata mota ƙirar Volkswagen Golf 3 ta taka bom ɗin a ƙauyen Yar Tasha.

Wani mazaunin Ɗansadau, Abdullahi Ɗansadau, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana cewa, “Wata mota ƙirar Golf 3 ce ta taka bam ɗin da safe, kuma ya fashe, ya kashe mutane shida nan take, ya kuma raunata wasu takwas.” Sai dai, CP Dalijan ya bayyana cewa mutum ɗaya ne kawai ya mutu, yayin da uku suka samu raunuka daban-daban.

Dalijan ya ce bincike na farko ya nuna cewa Lakurawa, waɗanda sojoji ke matsawa lamba su bar Nijeriya ne suka dasa bam ɗin. Ya kuma ƙara da cewa suna ƙoƙarin tserewa zuwa dajin Birnin-Gwari ta hanyar Zamfara. Ya yi kira ga jama’a su bayar da bayani mai amfani game da motsin waɗannan ‘yan ta’adda, yana mai jaddada cewa jami’an tsaro za su yi duk mai yiwuwa don murƙushe su. Wannan lamari ya biyo bayan wata fashewar bam makamanciyar wannan da ta auku a ranar Lahadi a ƙauyen Mai-Gungume, wanda ya kashe wani direban mota.