Daga BELLO A. BABAJI
Dakarun sojoji na Atisayen Birget na Musamman sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda shida a wani farmaki da suka kai wa mayaƙan Lakurawa a ƙaramar hukumar Gudu ta Jihar Sakkwato.
Wata takarda daga jami’in yaɗa labaran dakarun atisayen ‘Fansan Yamma’, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, ta ce atisayen ya kai ga ba-takashi tsakanin jami’an da mayaƙan inda sojoji biyar suka rasa rayukansu.
Jami’an sun yi nasarar ƙwato makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda huɗu alburusan 7.62mm guda 160 da kuma jakar alburusan 12.7mm.
Ganin haka ya sa rundunar ta yi kira ga mutane da su kasance masu sanya idanu akan abubuwan da ke kai-kawo a yankunansu.
Ta kuma yi kira a gare su da su ruwaito dukkan wani abin zargi da ke da alaƙa da ta’addanci ko kuma wanda zai haifar da tsaiko ga zaman lafiyarsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, haɗin kan al’umma yana da muhimmanci wajen kula da rayuka da dukiyoyinsu da jami’an suke ƙoƙarin yi a kowane lokaci.