Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Mashawarta ta Arewa (ACF) ta bayyana damuwarta kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ake kira da Lakuwara wadda ke addabar yankunan Jihohin Kebbi da Sakkwato a Arewa-maso-Yammacin Nijeriya.
Hukumomi a matakin yankuna da Hedikwatar Tsaro sun tabbatar da bayyanar ƙungiyar wadda ke tilasta a bi irin nata adalcin ta hanyar kashe jama’in tsaro na gwamnati da na gida, da kuma ɗaukar mabiya ta hanyar ba su kuɗaɗe ko bayyana manufofinsu.
Cikin wata takarda da Sakataren Labaran ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba ya fitar, ƙungiyar mashawartan ta ce ayyukan Lakuwara na ƙara ta’azzara taɓarɓarewar tsaro a shiyyar.
Ya yi nuni da harin da ƙungiyar ta kai a ƙaramar hukumar Argungu ta Kebbi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 acikin sa’o’i 48.
Lakuwara, wadda acikin ta akwai masu amfani da harsunan Faransanci da Larabci, ta na cigaba da ƙoƙarin samun ƙarin mambobi wanda hakan hatsari ne ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Don haka ne, ACF ta ke kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki, inda ta yi gargaɗi ga haɗarin da ke tattare da zuba wa lamarin ido, ta na mai bada misali da sadda aka samu ɓullar Boko Haram da wasu ayyukan ta’addanci da suka addabi shiyyar Arewa-maso-Gabas da Arewa ta Tsakiya.
ACF ta kuma yi kira da a yi nazari game da salon tsaro na ƙasa tare da inganta ƙoƙarin gwamnati na magance ire-iren matsalolin.
Har’ilayau, ACF ta jaddada muhimmancin aiki kafaɗa-da-kafaɗa tsakanin hukumomin tsaro da kuma gargaɗi ga masu tsegumi na taimaka wa ayyukan ta’addanci game da illar samuwar hakan acikin al’umma.
Kazalika, ƙungiyar mashawartan ta nemi a yi kwaskwarima wa jami’an haɗaka na MNJTF da roƙar ƙasashen maƙota musamman Nijar da su bada haɗin-kai wajen cimma nasara, inda ta bada misali da ziyarar da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya kai Nijar wanda za a iya amfani da ita wajen sabonta tsarin kula da kan iyaka da daƙile ayyukan ta’addanci.