Lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya (II)

*Manyan rashe-rashe a Kano
*Takarar Tinubu a mizani

Assalamu alaikum. Mai karatu barkanmu da sake saduwa a wannan fili na namu na saqonni, inda muke karɓar saƙonni game da abubuwan da suka shafi yau da kullum, waɗanda Allah cikin ikonsa ya ba ni ikon hangowa, kuma na ga ya kamata na ɗan wayar da kan jama’a a ciki.

In dai ana biye da mu, a makon da ya gabata na fara bayani ne game da mummuna bala’in nan da ake fama da shi a manyan makarantun ƙasar nan, inda ake samun Malamai suna lalata da ’ya’yan mutane don kawai su ba su maki, ko kuma don kar su kayar da su a jarabawa.

Wannann wani bala’i ne da yake tashe a yanzu a kusan duk waɗannan Jami’o’i da sauran manayan makarantun gaba da Sakandare da ke ƙasar nan, sai dai idan abin bai bayyana ba, amma abin ya zama ruwan dare.

A makon da ya gabata mun ce za mu ci gaba da bayyana ra’ayoyin jama’a game da waɗannan abubuwa, inda muka fara kawo maku wasu, a yau kuma za mu ci gaba cikin yardar Allah.
Wata ɗaliba daga Jami’ar ABU da ke Zariya, wacce kuma ta nemi a sakaye sunanta don wasu dalilai, wacce kuma ta ke matakin karatu na biyu, ta bayyana cewa, suna cikin tsaka-mai wuya a duk lokacin da suka ga wani Malami na neman wata alaƙa ta haɗa su.

“Gaskiya ko ni wani Malami ya yi ƙoƙarin jan ra’ayina kan wannan baɗala, duk da na yi ƙoƙarin fin ƙarfin zuciyata, sai Allah ya taimake ni a kai, na samu waraka a sakamakon wasu matakai da na ɗauka cikin hikima da suka haɗa da ɗaure wa Malamin fuska a duk lokacin da yake magana da ni, sai bai samu fuskar da zai sake nemana da wani abu marar kyau ba,” inji ta.

Ta ci gaba da bayyana cewa, “amma matsalar ita ce, wani lokacin gaskiya ana fin ƙarfin imanin ɗalibai mata ake yi, har a kai ga yin fitsara da su; misali, wasu ɗaliban za ka tarar suna faɗawa cikin tsananin buƙata, walau ta rayuwa ko ta wani abin da dole sai sun nemi agaji, hakan ya fi faruwa da ɗaliban da suke makarantar kwana, a irin wannan gaɓar ne ake samun nasara har a yi galaba a kan wasu ɗaliban mata.”

“Amma a wannan bigiren, ina bai wa ‘yan uwana ɗalibai mata shawara da cewar duk halin da ki ka tsinci kanki, walau na ƙarewar kayan abinci ne, ko kuɗin tafiyar da wasu abubuwan neman ilimi, to lallai ki daure ki yi haƙuri Allah zai kawo miki mafita, ba biye wa son rai wajen yin fasadi ba,” a cewarta.

Shi kuwa wani babban Malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Bauchi, Malam Hassan Hassan ya bayyana ra’ayinsa ne kan wannan batun da cewa, “a tunanina, ba rashin dokoki ne matsalarmu a ƙasar nan ba; akwai dokoki da dama, to amma ba ma amfani da su. Ma’ana, ba ma aiwatar da hukuncinsu. Sannan ga gazawar kotuna da fasadin Alƙalai.

Ya ci gaba da yin kira da cewa, “sannan kuma mu nemi gwamnatocin jihohi su aiwatar da dokar kula da yara ta 2013. Akwai sassa a cikinta wanda suke sa iyaye da Malamai da makarantu da kowa ya tashi akan himmarsa akan yara da aka ba su amana, idan kowa ya yi haka, to dukan matsalolin za su ragu ainun, ko ma su kare.”

Kamar kuma dai yadda muka sani cewa, a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Kaduna ta garqame wasu makarantun islamiyya a jihar domin zargin wasu malamai na cin zarafin ɗalibansu.

Hukumar Kula da Ingancin Makarantun na jihar Kaduna (KSSQA), ce ta rufe makarantun Islamiyyar biyu a jihar har sai masha Allahu kan zargin yi wa ɗalibai fyaɗe da yi wa wata ɗalibar ciki.

Shi kuwa Malamin Jami’a cewa ya yi illar yi wa ɗalibai fyaɗe a manyan makarantu matsala ce babba wacce ta ke buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe daga kowace ɓangare domin daƙile matsalar, inda ya yi nuni da cewa sanya doka mai tsauri ne kawai zai kawo raguwar matsalar.

Duk kuwa da cewa, wasu suna ganin matsalolin ba daga Malaman ne kawai ba. Misali, su ma yaran in aka yi rashin sa’a ba su samu tarbiyya mai kyau ba daga gidajensu, suna iya neman a yi lalata da su don buƙatarsu ta ƙashin kansu, walau ko don neman maki a bisa gandar karatu ko kuma don neman wani abu na duniya.

To, amma dai yin dokar zai taimaka kwarai wajen rage irin wannan aika-aikar, domin duk wanda ya san in an kama shi za a yi masa hukunci mai tsanani, to lallai ba zai taɓa yarda ya aikata ba.
Wassalam.

Daga Mahdi Musa Muhammad, marubuci kuma Ƙaramin Edita a Jaridar Blueprint Manhaja; 07066778190.

Haka nan kuma ga duk mai son tofa albarkacin bakinsa a wannan shafi na Wasiƙu, zai iya aiko da saƙo ta imel ɗimnu kamar haka; [email protected] ko [email protected]

Manyan rashe-rashe a Kano

Shin Kanawa ne a kai ma rashi ko kuma ƙasarmu da sauran al’umma? Allah ka jiƙan waɗancan mutane tun daga Dr Ibrahim Datti wanda shugaba ne a majalissar ƙoli ta harkokin Musulunci a Nijeriya. Kuma ya jarraba neman zamowa shugaban ƙasa a Jam’iyyar SDP a shekurun baya. Marigayi Dr Datti Ahmad ya bar duniya a ranar 30-12-2021 kwanaki kaɗan, sai kuma Alhaji Bashir Othman Tofa wanda a shekara ta 1993 a jam’iyyar NRC yai takara ta neman shugabancin ƙasa wanda a gefe guda Jam’iyyar SDP ta tsayar da Chief MKO Abiola wanda a cikinsu duka babu wanda ya yi shugabancin duk da kasancewa Chief MKO Abiola ne mai rinjayen kuri’u.

Bashir Tofa

Rasuwar Dattijon malami Dr Ahmad Bamba BUK ita ma ta zo ne a daf-da-daf wato ƙasa ga makonni biyu a tsakaninsu dukka ukun. Haƙiƙa Kanawa ba ku kaɗai wannan rashi ya shafa ba abu ne wanda ya gamo sauran al’umma. Allah ka gafarta musu, ka kyautata makwancinsu. Mu kuma ka kyautata tamu idan ajali ya zo.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina; 07066434519, 08080140820

Takarar Tinubu a mizani

Ta tabbata cewa jagaba ya bayyana manufarsa tun wuri dangane da neman fitowa yin takara ta shugabancin Nijeriya a 2023. Ko shakka babu akwai ababe na lura dangane da wancen lamari duk da cewa wasu za su ga tamkar hakan ba zai yiwu ba.

Chief Tinubu

Amma ni a tawa ’yar fahimta ban ga laifin Tinubu ba domin idan muka nutsu mu ka yi waiwaye a lamarin Tinubu tun a zaɓen fitar da ɗan takara a 2014 mun tabbatar ƙabilar Yarbawa sun ba Buhari goyon baya. Haka a zaɓen 2015 da na 2019 duka mun san Yarbawa sun zaɓi Buhari. Wannan ke iya nuna mana cewa a Arewa ne aka fi yin siyasa ta gaba ta fushi da fushin wasu. Haka yarfe da hassada ta siyasa duk an fi samun ta a Arewa duk kuwa da cewa a kudanci a na da jam’iyyu amma a zaɓe dunƙulewa su ke. Shawara ta ga talakawa ita ce addu’a da duba cancanta.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina; 07066434519, 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *