Lamash ya miƙa wa Triumph kashi 25 cikin 100 na shagunan da ya gina

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Kamfanin Lamash ya gina kasuwar musayar kuɗi ta zamani a tsohon offishin kamfanin buga jaridar Triumph, Albishir da kuma jaridar Ajami ta Hausa, inda yanzu haka kamfanin na Lamash ƙarƙashin jagoranci Hadiza Abdulkadir da ta wakilci kamfanin wajen mika wa kamfanin Triumph kashi 25 cikin na shagunan da ya gina a tsohon ofishin Triumph dake unguwar Fagge a Kano.

Hajiya Hadiza Abdulƙadir ta bayyana haka ne a lokacin taron miƙa shaguna 64 ga shugaban kamfanin Triumph ƙarƙashin shugabancin MD Alhaji Lawan Sabo, a taron da aka yi a tsohon kamfanin Triumph a ranar Larabar da ta gabata.

Hadiza Abdulƙadir ta ce wannan ce ranar da aka cika alƙawarin yarjejeniya da kamfanin ya yi da gwamnatin Kano na cewa za a gina wa kamfanin Triumph mazauni a gidajen Amana City dake kan hanyar Zariya kuma an gina, sai kuma na biyu na bada kashi 25 na shagunan da Lamash ya gina a tsohon matsugunin Triumph a wannan yarjejeniya mai suna PP kamar yadda aka san tsarin irin wannan yarjejeniya da gwamnati akan aiki irin wannan na cigaba.

A ƙarshe shi ma shugaban kamfanin Triumph MD Alhaji Lawan Sabo kuma babban Editan rukunin jaridun na Triumph da jaridar Albishir ta Hausa da Hausa Ajami ya tabbatar da karvar makullan shagunan kashi 25 na shagunan wannan kasuwa ta musayar kuɗaɗen waje ta zamani wato Beureu De Change wanda waɗannan shaguna suka zama mallakar kamfanin buga jaridun Triumph, na gwamnatin Kano.

Sabo ya ce: “Wannan babban cigaba ne, kuma zai ba kamfanin Triumph damar riqe kansa har da siyo injinan aiki a wannan kamfani na Triumph kuma Ina so sabuwar gwamnati da tsohuwar gwamnati cewa Allah ya sani farkon wannan aiki na nuna vacin rai na har ma ana ganin ina rigima da gwamnati ne amma kuma yanzu wannan abu ya zama cigaba kuma zamu zauna da duk wanda ya kamata wajen tattauna wannan al’amuran domin samun nasara,” a cewar Malam MD Lawan Sabo.