Daga BELLO A. BABAJI
Wata babbar kotun tarayya dake Legas, ta haramta wa Hukumar Kiyaye Haɗdura (FRSC) kama motoci masu koɗaɗɗun allunan lambobi.
Mai Shari’a Akintayo Aluko ya bayyana hakan a ranar Juma’a inda ya kuma hana hukumar karɓar tara ko hukunta direbobin da ke ɗauke da motoci masu koɗaɗɗun lambobi.
Kotun ta bada umarnin ne a lokacin da ta ke hukunci game da wata ƙara da wani lauya mai suna Chinwike Chamberlian Ezebube ya shigar akan FRSC.
Ya shigar da ƙarar ne akan hukumar don kotun ta bayyana ko FRSC ta na da alhakin hukunta masu koɗaɗɗun allunan lambobi a motocinsu ko cin su tara.
Saidai lauyan da ke kare wanda ake ƙara, B.O Nnamani ya gabatar da takardar da ke neman kotun ta yi watsi da ƙarar.
A lokacin da ya ke gabatar da hukunci, Allƙali Aluko ya ce babu wata hujja ta mayar da amfani da koɗaɗɗen allon lamba a matsayin babban laifi a dokance, ya na mai haramta karɓar tara ko hukunta direbobi akan haka.