Lauyoyi da dama ba su san me sabon ƙudurin haraji ya ƙunsa ba – Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa mafi yawan lauyoyi, har da wasu ‘yan majalisa, ba su fahimci abubuwan da dokokin gyaran haraji suka ƙunsa ba. A cewarsa, an hanzarta muhawarar dokokin zuwa karatu na biyu ne domin a bai wa al’umma damar tattaunawa da bayar da sharhi akansu.

Dokokin gyaran harajin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki a farkon watan Satumba sun haifar da cece-kuce, musamman daga yankin Arewa, inda ake ganin dokokin na iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki a yankin. Gwamnonin Arewa, sarakunan gargajiya da wasu ƙungiyoyi sun yi watsi da dokokin, suna masu cewa suna da illa ga yankin da ƙasa baki ɗaya.

Da yake tsokaci kan batun, Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, a wata hira da BBC Hausa, ya bayyana damuwarsa kan yadda dokokin suka samu wucewa cikin gaggawa a Majalisar Dokoki. Ya ce, idan aka zartar da dokokin, gwamnonin ba za su iya biyan albashi ba. Sai dai Sanata Barau ya ce an wuce da su karatu na biyu ne don a bai wa ‘yan Najeriya damar fahimta da bayar da ra’ayinsu kafin a ɗauki mataki na gaba.

Sanata Barau ya ƙara da cewa, “Dole sai dokokin sun tsallake karatu na biyu kafin a kai su kwamitoci don duba su. Wannan ne ya bai wa kwamitocin damar bincike da yin nazari. Hakan na nufin karatu na biyu ba ƙarshen tsari ba ne, sai ma farkon mataki ne. Ana so ne al’umma su samu damar yin tambayoyi, bayar da gudunmawa da kuma yin ƙorafi idan akwai.” Ya kuma bayyana cewa za a gayyato ƙwararru su yi nazari kan dokokin domin a tabbatar da cewa ba za su cutar da al’umma ba.