Lawal ya ƙaddamar da raba kayayyakin karatu ga makarantu 250 a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwanna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada cewa fannin ilimi shi ne kan gaba a jerin ɓabgarorin da zai bai wa fifiko wajen gina jihar Zamfara.

Lawal ya bayyana haka ne a wajen bikin ƙaddamar da raba kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantu wanda ya gudana ranar Laraba a Gusau, babban birnin jihar.

Rabon kayayyakin ya shafi makarantun gwamnati 250 ne da suka haɗa firamare da ƙananan sakandare a jihar.

Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris ya ce, Hukumar Ilimin Bai-ɗaya (UBEC) da ke Abuja da kuma UNICEF su ne suka samar da kayayyakin.

Sanarwar da Idris ya fita ta ce, makarantun gwamnati 250 ne za su ci gajiyar tallafin. Kuma kayayyakin da za a raba sun haɗa da litattafan karatu 242,176 haɗa da kujeru da tebura da sauransu.

Yayin ƙaddamar da shirin, Gwamna Lawal ya ce Jihar Zamfara za ta ci gaba da neman tallafi a gida da waje domin bunƙasa sha’nin ilimi a jihar.

Ya ce, “Na yi farin cikin ganina a wannan taro na raba kayayyakin karatu ga ɗalibai. Wannan na ɗaya daga cikin tallafi da daman da Zamfara ta samu.

“Muna aikin gyara a makarantu sakandare guda 60 a sassan jihar ƙarƙashin tallafin Bankin Duniya da shirin bunƙasa rayuwa, CSDA.

“Akwai makarantu guda 6 da ake yi wa kwaskwarina a kowace ƙaramar hukuma, yayin da Gusau, babban birnin jihar ke da guda 8,” in ji Gwamnan.

Kazalika, ya yi ƙarin bayani kan yadda gwamnatinsa ke ci gaba da ƙoƙarin inganta fannin ilimin jihar wanda daga cikin matakan da ya ɗauka har da biyan bashin da hukumomin shirya jarrabawa na WAEC da NECO ke bin jihar tun a gwamnatin da ta gabata da sauransu.