Legas kaɗai na da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi milyan 4, cewar Marwa

Daga WAKILINMU

Shugaban Hukumar Yaƙi da sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) Janar Muhammadu Buba Marwa, ya ce aƙalla mutum miliyan 4 da rabi ke mu’amala da miyagun ƙwayoyi a birnin Legas, abin da ke nuna ƙaruwar matsalar da ta addabi ƙasa baki ɗaya.

Yayin da ya ke ziyarar gani da ido tun bayan naɗa shi a matsayin shugaban hukumar, Marwa ya bayyana birnin Legad a matsayin jihar da ake samun kashi 30 na masu amfani da miyagun ƙwayoyin.

Ya ce daga cikin mutane miliyan 15 da aka yi ƙiyasin suna mu‘amala da miyagun ƙwayoyin wajen sha da fataucin su, miliyan 4 da rabi na da zama a Lagas ne, yayin da sauran ke a sassan ƙasa.

Janar Marwa ya bai wa jami’ansa umurnin matse ƙaimi wajen shawo kan matsalar musamman ganin an kama tare da hukunta masu safarar ƙwayar da kuma masu sayar da ita.

Marwa ya danganta matsalar Legas da yawan gidajen sayar da magunguna waɗanda ba su da rajista da hukumar da yawan su ya kai kusan miliyan guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *