Legas: NAFDAC ta rufe kamfani mai sayar da kayayyakin da wa’adin amfaninsu ya ƙare

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta rufe wani kamfanin sarrafa abinci a Jihar Legas bisa laifin sayar wa jama’a da sinadarin haɗa abinci (Thyme da Curry) bayan kuma wa’adin amfaninsu ya ƙare.

NAFDAC ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin tsaftace Nijeriya daga abinci mara inganci domin ci gaba da kare lafiyar ‘yan ƙasa.

A sanarwar da jami’in yaɗa labarai na shiyya na hukumar Sayo Akintola ya fitar, Babbar Daraktar hukumar Prof. Mojisola Adeyeye ta bayyana damuwarta kan lamarin.

Tana mai cewa za a ƙaƙaba wa kamfanin da lamarin ya shafa takunkumi bisa laifin cutar da lafiyar ‘yan ƙasa.

Sanarwar ta nuna cewa biyo bayan kwarmata wa hukumar abin da ke faruwa a kamfanin, daga nan jami’ansu suka sunkuya bincike kan harkokin kamfanin Every Rose Limited mai sarrafa sinadaran haɗa abinci a sassan Legas inda suka gano tarin sinadari ‘Curry’ da ‘Thyme’ a rumbun ajiyar kamfanin da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen sabunta bayanin sinadaran waɗanda wa’adin amfaninsu ya rigaya ya ƙare.

Adeyeye ta ce rassa guda biyu na kamfanin da suka ziyarta an rufe su tare da dakatar da su daga ci gaba da harkokinsu. Sannan jami’an kamfanin waɗanda aka same su dumu-dumu suna aikin sabunta bayanan sinadaran an kama su, an tafi da su ofishin hukumar don zurfafa bincike.

Bayanan NAFDAC sun nuna kamfanin da lamarin ya shafa yana sarrafa abubuwa da dama masu ɗauke da taken SOMGEO, inda yakan sarrafa garin tafarnuwa da curyy da thym da garin citta da dai sauransu, wanda wa’adin amfanin kayayyakin ya ƙare tun a ranar 5 ga Disamban 2017.

“A shirye muke mu yaƙi kayayyaki marasa inganci a kasuwanninmu domin kare lafiyar ‘yan ƙasa”, inji Adeyeye.