Legas: Sojojin sama sun kama mutum 9 kan zargin satar mai da ƙwato buhunan tabar wiwi

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an sansanin sojojin sama na NNF Beecroft, sun yi nasarar kama mutane tara da ake zargin ɓarayi ne da ke satar mai, da kuma ƙwato buhuna 28 na tabar wiwi masu nauyin 756kg a yayin atisayen yankunan ruwa dake Jihar Legas.

Jami’an sun kama mutanen ne a ranakun 10 da 11 ga watan Fabrairu a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan satar mai da safararsa da sauran nau’ukan manyan laifuka a bakin ruwa.

Hakan na zuwa ne sakamakon umarnin da shugaban sojojin sama ya bayar na dakatar ire-iren munanan laifukan daga shekarar 2023 zuwa 2026.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Laraba, Kwamandan rundunar, Komodo Paul Ponpa Nimmyel ya ce jami’an sun gudanar da atisayen ne bayan samun wani bayanin sirri daga Cibiyar kula da shiyyar Yamma ta rundunar, wato FEA.

Ya ce sun kama mutanen ne a lokacin da aka samu labarin wani jirgin ruwa na katako da ake zargin ɓata-gari ne suke jigilar sa da nufin tafiya da shi Jamhuriyar Benin.

A lokacin da jami’an suka cimma jirgin, sun yi nasarar kama mutane bakwai da wasu duro-duro guda 408 da na’urar tuƙa-tuƙa uku da injinan Yamaha 40HP guda takwas.

Ya bayyana nasarar a matsayin abinda ya dakatar da asara mai girma a tattalin ƙasa saboda yiwuwar gudanar da ayyukan satar mai da makamantansa.

A wani labarin, jami’an sun kama mutane biyu da ake zargin su da hannu a safarar tabar wiwi a ranar Litinin, ɗauke da injin Yamaha 40HP a Topo dake yankin Badagry.

Wata majiya ta tabbatar da cewa an kira mutane biyun ne da nufin kai kayayyakin ga waɗanda ke ayyukan safarar kayan sata a teku.