Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Leicester City ta ƙasar Ingila, ta naɗa tsohon kocin PSV Eindhoven, Ruud Van Nistelrooy a matsayin sabon mai horar da ƴan wasanta.
Ɗan ƙasar Holand ɗin ya maye gurbin Steve Cooper ne wanda ƙungiyar ta sallame shi a makon da ya gabata bayan wasanni 12 a gasar Firimiyar bana.
Van Nistelrooy ya rattaɓa hannu a kwantiragin shekaru biyu da rabi inda wa’adinsa zai ƙare a watan Yunin 2027.
Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan ajiye aikinsa na koci mai riƙon ƙwarya a Manchester United sakamakon zuwan Ruben Amorim.
Ya bayyana jin-daɗinsa game da zuwan nasa ƙungiyar, ya na mai cewa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya dawo da martabarta wadda a yanzu ta ke na 16 a tebur.