Lewandowski ya ci ƙwallonsa na 100 a Gasar Zakarun Turai

Robert Lewandowski ya zama ɗan wasa na uku da ya zura ƙwallaye 100 a gasar kofin zakarun Turai yayin da Barcelona ta lallasa Stade Brestois da 3-0 a wasan da suka fafata ranar Talata.

Cristiano Ronaldo ne kawai mai ƙwallaye 141 da Lionel Messi mai 129 suka fi ɗan wasan mai shekaru 36 a yawan ƙwallaye na gasar zakarun Turai.

Lewandowski ya zura ƙwallonsa ta 100 a minti na 10 da fara wasa, kuma shine ya ci ƙwallye biyu cikin ukun da ƙungiyar ta yi nasara.

Dani Olmo kuwa ya ci wa Barcelona ƙwallonsa ta farko a gasar cin kofin zakarun Turai.

Barcelona ta koma matsayi na biyu a teburin gasar da maki 12, bayan ta yi nasara a wasanni huɗu cikin biyar, yayin da Brest ta koma matsayi na tara.