Li Keqiang: Ƙofar Sin a buɗe take tare da maraba da baƙi daga ɓangarori daban-daban

Daga CMG HAUSA

A jiya ne, Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da ‘yan jarida tare da shugabannin manyan hukumomin tattalin arzikin duniya dake halartar taro na 7 na rukunin “1+6” a birnin Huangshan na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.

Li Keqiang ya bayyana cewa, taron ya yi imani da tabbatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban daban, da inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Sin ta samu moriya daga manufar bude kofa ga kasashen waje, don haka ta himmatu wajen aiwatar da manufar, kana tana martaba odar kasa da kasa da ka’idojin tattain arziki da cinikayya, Sin tana goyon bayan manyan hukumomin tattalin arzikin duniya guda shida da su taka muhimmiyar rawa wajen fadada bude wa juna kofa a duniya.

Shugabannin manyan hukumomin tattalin arzikin duniya da suka halarci taron, sun nuna yabo ga muhimmiyar rawa da taron ya taka, sun bayyana cewa, Sin tana da kyakkyawar makomar bunkasuwar tattalin arziki, sun kuma ji dadin ganin yadda Sin take fadada bude kofa ga kasashen waje, da yin maraba da yadda Sin ta kyautata matakan yaki da cutar COVID-19, kana sun yi imani da cewa, hakan zai sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin Sin da na duniya baki daya, suna kuma son zurfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakaninsu da kasar Sin.

Mai fassara: Zainab

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *