Daga USMAN KAROFI
Biyo bayan hukuncin da hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta yanke kan ƙorafin da hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta gabatar kan rashin adalcin da aka nuna wa tawagar Super Eagles a ƙasar Libya, wasu ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar sun bayyana cewa an fara kama su da cin tarar masu zaman ba bisa ƙa’ida ba a can.
An tsare tawagar Super Eagles na tsawon sa’o’i 20 a filin jirgin Al-Abraq da ke gabashin Libya bayan sun isa don buga wasan kofin zakarun Afirka (AFCON) na shekarar 2025 tsakaninsu da tawagar Libya. Asalin wurin da aka tsara jirgin su zai sauka shi ne filin jirgin Benghazi, daga nan za su yi tafiyar kusan awa huɗu zuwa Benina domin gudanar da wasan.
To sai dai, kafin su isa, an umurci matuƙin jirgin da ya sauka a Al-Abraq, wanda ke da tazarar mil 150 daga asalin wurin da za su je. Wannan al’amari ya jawo cece-kuce da takaici, lamarin da ya sa NFF ta janye tawagar daga wasan sannan ta shigar da ƙara a CAF.
A hukuncin da aka fitar a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, hukumar CAF ta baiwa Super Eagles maki uku da ƙwallaye uku bisa laifin rashin bin doka da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Libya (LFF) ta yi. Haka kuma, an ci tarar Libya kuɗi dalar Amurka $50,000 a matsayin diyya, wanda za a biya cikin kwanaki 60.
Bayan sanarwar CAF, shafin labarai na Libya News Today,wanda ke da mabiya kusan 188,000, ya wallafa cewa gidajen talabijin na Libya na kira ga gwamnati ta fara kamawa da cin tarar ‘yan Nijeriya masu aiki ba bisa ƙa’ida ba a ƙasar. An bayyana cewa ‘yan Najeriya za su biya tarar $500 kafin a basu takardar izinin zama a ƙasar.