Lifidi Foundation ta tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi sama da mutane 300 a Kafancan

DAGA ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan

Wata ƙungiya mai zaman kanta a garin Kafanchan Jihar Kaduna mai suna ‘Lifidi Jama’a Charity Foundation’, ta tallafa wa masu karamin ƙarfi sama da mutum 300 da jalin da za su fara kasuwanci.

Bikin tallafin da aka gudanar a kofar Fadan Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu a cikin Wannan sati, ya kasu ta hanyoyin tallafin kayayyakin sana’oi daban-daban, kuɗaɗe da kuma babura ga ƙungiyoyin tsaro na sa-kai.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin bikin, shugaban Lifidi Charity Foundation kuma Lifidin Jama’a, Alhaji Bashir Idris yace, wannan yunƙurin da ya yi domin ya taimaka wa masu ƙananan ƙarfi ne waɗanda sana’oinsu na kullum bai taka kara ya karya ba, domin su sami hanyar bunƙasa harkarsu, har ta kawo ci gaba a rayuwarsu.

Alhaji Idris ya qara da cewa, hanyar da ya gani kenan wadda ta dace da zai bada gudummuwa wajen tallafa wa mabuƙata domin rayuwarsu ta inganta, a wannan dalili ya yi kira da babban murya ga masu hannu da shuni su zo a haɗa hannu a taimaki wa masu kananan ƙarfi, gajiyayyu da mabuƙata.

Da farko Babban bako a wurin taron, Farfesa Sale Momale ya yaba wa Lifidi Foundation saboda wannan jajirce wanda suka yi na tallafa wa kama’a mabuƙata.

Alhaji Sale yayi kira ga ƙungiyar da ta faɗaɗa abi nda ta ke yi saboda mutane da yawa su amfana, tare da sake yin kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da abinda Lifidin Jama’a yakeyi domin a tallafa wa mabuƙata da yawa saboda a rage zaman banza da talauci a ƙasa.

Bayan yayi wa ƙungiyan addu’an fatan alkhairi da ci gaba, Alhaji Momale ya ƙalubalanci waɗanda aka basu tallafin da, su yi la’akari da cewa an tallafa musu ne saboda su yi amfani da daman domin kyautata wa rayuwarsu.

A nasa jawabi, Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu ya sanya wa ƙungiyan Lifidi Jama’a Charity Foundation albarka, ya ƙara kuma da jaddada goyon bayansa ga ƙungiyar.

Waɗanda suka sami tallafin, sun haɗa da maza da mata daga ɓangaren Muslmai da Kiristoci daga kowane lungu da saaon Ƙaramar Hukumar Jama’a.