Likitoci sun fara yajin aikin gargaɗi a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA) reshen Jihar Nasarawa, ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyar bayan da gwamnati ta gaza wajen cim ma buƙatun mambobinta.

Shugaban NMA a jihar, Mr. Peter Attah, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a garin Lafia, babban birnin jihar.

Ya ce sun yanke shawarar tafiya yajin aikin ne a wajen taron da ƙungiyar ta shirya a ranar Talata.

Yana mai cewa, gwamnati ta gaza wajen cim ma buƙatunsu a cikin wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyar ta ƙayyade mata farawa daga ranar 13 ga Yuni, 2023.

Ya ƙara da cewa, daga cikin dalilan da suka haifar da yajin aikin nasu har da batun rashin ƙarin girma ha likitoci, rashin ƙarin albashi na shekara-shekara, rashin biyan mafi ƙarancin albashi da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *