Likitoci sun gano kuɗaɗe da ƙusoshi a cikin wani mutum

Likitoci sun shiga mamaki bayan sun gano ɗaruruwan tsabar kuɗi da ƙusoshi da batura da guntattakin gilasai bayan da wani mutum mai suna Burhan Demir daga garin Ipekyolu na ƙasar Turkiyya ya kai ƙaninsa asibiti saboda kukan ciwon ciki.

A lokacin da likitocin suka yi gwajin hoton cikin mutumin ta amfani da ‘Endoscopic’ tare da ɗaukar hoton cikin da na’urar d-ray sun yi mamaki bayan gano abubuwa 233 a cikin mara lafiyar mai shekara 35.

Abubuwan sun haɗa da tsabar ƙarafan kuɗin ƙasar Lira guda ɗaya da batura da mayen ƙarfe da ƙusoshi da gilasai da duwatsu.

Daga baya likitocin sun cire abubuwan da suke cikin majinyacin, mai suna Z, kawai.

Wani likitan fida mai suna Dokta Binici, ya ce, “a lokacin tiyatar, mun ga ɗaya ko biyu daga cikin ƙusoshi sun bi ta bangon cikinsa.

“Mun gano cewa a cikin babban hanjinsa akwai ƙarafuna biyu da duwatsu biyu masu girma daban-daban.

“mun gano cewa akwai batura da mayen ƙarfe da ƙusoshi da tsabar kuɗi da guntayen gilasai. Mun cire dukkan abubuwan daga cikinsa gaba ɗaya.

“Ba yanayin da muke gani a manya ba ne, yawanci a cikin yara ne da suke haɗiye abubuwa ba tare da saninsu ba. Ana iya ganin hakan a cikin marasa lafiya masu tavin hankali ko fursunoni ko waɗanda ake cin zarafinsu a cikin rukunin manya,” inji shi.

Burhan ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na ƙasar cewa, “an kai ƙaninsa wannan asibiti ne bayan binciken lafiyarsa da aka yi, an yi masa tiyata aka cire waɗannan abubuwa daga cikinsa.

Ba a dai bayyana lokacin da aka gudanar da aikin ba, amma an bayar da labarin a kafafen yaɗa labarai na ƙasar a ranar 15 ga watan Yunin bana.

Burhan ya ƙara da cewa, “na gode wa likitocin saboda kulawa da goyon bayansu.”