Likitoci sun tsagaita yajin aiki don lura da gudun ruwan gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar likitoci da aka fi sani da NARD a taƙaice, ta tsagaita yajin aikin gama garin da take yi na tsawon makonni shida domin bai wa Gwamnatin Tarayya damar biya mata buƙatunta.

A jiya Litinin NARD ta ba da sanarwar tsagaita yajin aikin da ta shafe kwanaki 64 ta na yi, kamar yadda shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr Godiya Ishaya, ya bayyana a tattaunawar da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya yi da shi a Abuja.

Ishaya ya ce ƙungiyar ta ɗauki matakin tsaigaita yajin aikin ne duba da ƙoƙarin da ta ga gwamnati na yi don cimma buƙatunta.

Ya ce muddin gwamnati ta iya cimma buƙatunta cikin makonni shida da ta ɗibar mata, ka iya yiwu ta janye yajin aikin nata baki ɗaya.

A cewar Ishaya, “Ba wai mun janye yajin aikin ba ne baki ɗaya, mun tsagaita ne na makonni shida don bai wa gwamnati damar yin abin da ya dace.

“Idan gwamnatin ta iya aiwatar da abin da ya kamace ta a cikin makonni shida, daga nan za mu zauna mu duba mu ga mataki na gaba da ya dace mu ɗauka.

“A farkon wannan shekara aka cimma yarjejeniya tsakanin NARD da Gwamnatin Tarayya, rashin aiwatar da yarjejeniyar ya sa muka tsunduma yajin aiki.”

Kazalika, Ishaya ya ce ƙoƙarin da suka ga gwamanti na yi a yanzu wajen bai wa yarjejeniyar da ke tsakani muhimmanci, ya sa shugabannin ƙungiyar suka yi taron gaggawa inda a nan suka cimma matsayin sassauta matakin yajin aikin nasu.

Buƙatun da NARD ta nema a wajen gwamnati sun haɗa da; biyan da ƙarin alawus-alawus da kashi 50 ga ma’aikatan kiwon lafiya, da biyan bashin alwus na yaƙi da cutar korona da suke bi, da biyan inshorar ma’aikatan da suka rasa ransu a bakin aiki a dalilin yaƙi da cutar korona da dai sauransu.

Tun bayan da likitocin suka soma yajin aiki a watan Agustan da ya gabata, asibitocin gwamnati a matakin tarayya da jihohi suka shiga garari saboda rashin likitocin da za su kula da marasa lafiya.