Likitocin ƙasar Sin sun gudanar da bita ga takwarorinsu na Saliyo game da yaƙi da cutar Malaria

Daga CMG HAUSA

Likitocin ƙasar Sin dake aiki a Saliyo, sun gabatar da bita ta musamman game da matakan kandagarki, da magance cutar zazzabin cizon sauro ko malaria ga likitocin ƙasar.

Yayin bitar ta jiya Alhamis, wadda aka gudanar a asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, jagoran tawagar likitocin na Sin Zhan Xinjie, wanda kwararre ne a fannin gwaje gwajen cututtuka, ya gabatar da maƙala game da cutar ta Malaria, da nau’o’in sauro dake baza ta a sassan duniya daban daban, inda kuma ya yi fashin baƙi game da dabarun gano cutar da ake amfani da su a ɗakunan binciken ƙwayoyin cuta.

A cewar Zhan Xinjie, burinsu shi ne zurfafa fahimta game da cutar, tare da aiki kafaɗa da kafaɗa, wajen inganta ayyukan kandagarki da magance cutar ta hanyar samar da horo.

A nasa ɓangare kuwa, ɗaya daga likitocin Saliyo dake aiki a asibitin Sallieu Kamara, godewa likitocin ƙasar Sin ya yi bisa yadda suka tsara cikakken horo ga takwarorinsu na Saliyo.

Yana mai cewa, ilimin da suka koya zai taimaka musu wajen gaggauta gano cutar ta malaria.

Kamara ya ce har yanzu, asibitin nasu na da ƙarancin kayayyakin aiki na binciken cutar, don haka ya gabatar da roko ga ɓangaren na Sin, da ya ci gaba da tallafawa.

Ya ce “Ƙwarewa da muke samu ta hanyar horas da jami’an lafiya, na taka rawar gani wajen kuɓutar da rayukan ƙarin al’ummar mu”.

Mai fassara: Saminu Alhassan