Likitocin Maradona na fuskantar shari’a shekaru huɗu bayan mutuwar ɗan wasan

An fara sauraren ƙarar likitocin Diego Maradona kan dalilin mutuwar tsohon gwarzon ɗan ƙwallon Argentina a birnin Buenos Aires.

Maradona yana murmurewa daga jinya a lokacin da ya mutu sakamakon ciwon bugun zuciya a 2020, yana da shekara 60 da haihuwa.

Lokacin yana samun sauƙi a gida, bayan tiyata da aka masa da ta kai an cire masa gudan jinin da ya taru a ƙwaƙwalwarsa a watan.

Masu shigar da ƙara sun ce za a iya ceton ran Maradona a lokacin, an zargi ma’aikatan lafiyar da yin sakaci.

Sai dai waɗanda ake ƙara sun ce Maradona ne ya ƙi yadda a ci gaba da kula da lafiyarsa, ya kamata ya ci gaba da zama a asibiti, bayan da aka yi masa tiyata.

Za a iya ɗaure su a gidan yari tsakanin shekara takwas zuwa 25 da zarar an same su da laifi, wato tuhumar “kisan kai da yiwuwar niyya”.

Fiye da mutum 100 za su bayar da shaida da ake sa ran saurara har zuwa cikin Yuli.

Ana kwatanta Diego Maradona ɗaya daga fitattun ’yan wasan tamaula a duniya, wanda ya yi ƙyaftin ɗin Argentina da ta lashe kofin duniya a 1986.

Daga baya Maradona ya faɗa shan koken da ta kai an dakatar da shi wata 15, bayan da aka same shi da laifi a 1991.

Lokacin da aka samu labarin mutuwarsa, masu bibiyar tamaula a duniya sun kaɗu, inda aka shiga alhinin rashinsa, kuma dubban magoya baya suka taru a fadar gwamnati a Buenos Aires.