Litar fetur: Za a ƙara wa barkono zafi

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya ba a ɗaukar raɗe-raɗi ko jita-jita kan ƙarin farashin man fetur da wasa don yadda ƙarin ke neman zama ruwan dare game duniya a Nijeriya. Ko ma’aikata sun tafi yaji don fusata da ƙarin farashi tamkar yaji za a ƙara wa yaji.

In dai ba gwamnati za ta ɗau wasu matakai masu tasiri na kawo sassauci ba ta hanyar sa ido kan yadda farashin ke tafiya ɗawainiya ce kawai za a yi ta sha. Ai tun da gwamnati ta cire dukkan tallafin fetur ba wata dabara ta yanzu-yanzu da ta wuce zuba ido kan ’yan kasuwa kar su ninka riba. Da farko mun fahimci an bar kasuwa ta yi halin ta ko a ce an sanya kamar gasa tsakanin ’yan kasuwar kowa ya kawo ya sayar a farashin da jama’a za su fi saya har farashin ya sauko. Ba na ganin akwai ɗan kasuwar da zai iya tafiya da ƙaramar riba a zamanin yau.

In ma an ce ƙaramar ribar ce to dama ’yan kasuwar na da ƙungiyar su da su ke amfani da ita wajen fitar da matsaya. Ɗan kasuwa ɗaya ba zai sayar da hajar ta yi bambancin da saura ba haka su ke sayarwa ba. Duk mai kwatanta litar fetur da yadda farashin layin wayar salula ya riƙa saukowa har ya zama tamkar kyauta bai yi dogon nazari ba ne.

Kamfanonin sadarwa na da bambancin da ’yan kasuwar man fetur. Mu duba tarihin farashin mai a tsawon duk shekaru mu ga baya ya kan komo ko kullum sama ya ke cillawa? A rubutun da na yi kan qarin farashi a baya na kawo hasashen masu cewa ’yan jari hujja na da zummar sai litar fetur ta koma naira dubu ɗaya. Kuma maganar su ba ta da nisan gaske daga gaskiya musamman in an duba yadda a ka wayi gari ’yan kasuwar ba sanarwa sun cilla litar sama.

Fatar ma da a ke yi yanzu ba litar ta dawo yadda ta ke a baya ba ne, a’a, aƙalla ta komo Naira 600 ko dai in an yi sa’a Naira 550. Idan ƙunci ya yi yawa a kan nemi ɗan sauƙi-sauƙi ne ko yaya ya ke don a iya ɗan tagazawa ko za a iya kai wa gaci. Da babu gara ba daɗi. Zai iya yiwuwa ka ga farashin wani kayan masarufi ya yi tsada amma ba zai dami dukkan jama’a ba ko a ce talakawa misali a ce farashin nama, kifi ko koyi da sauran sun a more rayiuwa ba za su tayar da hankalin akasarin jama’ar da dama sai a shekara su kan samu ɗaya daga waɗannan abubuwan ba, amma da zarar an ce litar mai ta tashi to ka tabbatar talaka zai ji a jikin sa don masara da yin miya lami ma sai ya gagara.

Sufuri na tafiya nan zuwa can don neman na cefane sai ya faskara. Ko yanzu ai farashin masara ya tashi har an fara samun labarin matsalar nan ta satar hatsin da a ka kai nika inji ta fara dawowa. Rannan ina cikin shiri da matasa a Danko Wasagu da ke jihar Kebbi sai wasu su ka ce har tafasa mutane su ka koma su na ci. Ina cikin mamaki sai na ji wani malami na cewa tafasar ma ta kare.

Idan an rasa abincin kyauta irin tafasa, rama da yaɗiya ai an kusa kai wa gargara kenan sai mu yi ta addu’ar samun sauqi daga wajen Allah. Gaskiya dabarar mutane ba za ta kai ko ina ba sai an haɗa da neman taimakon Ubangijin sammai da ƙassai.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nuna damuwa ga yadda darajar Naira ke ƙara yin ƙasa in an zo canjin dala.

Naira dai ta yi matuqar sulmuyowa ƙasa iye da kowane lokaci a tarihi inda ta kai Naira 950 kan dala ɗaya tal duk da a yanzu kasuwar ta nuna dalar ba ta da farashi ɗaya har ta sauko ƙasa da Naira 900 har ma wasu ke yayata an samu faɗuwar dalar.

Dalilin hakan ya sa shugaban ya gana da muƙaddashin gwamnan babban banki CBN Folashodun Sonubi a fadar Aso Rock. Shugaban ya buƙaci Sonubi ya gano duk hanyar da za a bi wajen daidaita farashin Naira ko ma a ce dawo da darajar Nairar.

Da ya ke zantawa da manema labaru bayan ganawar, Sonubu ya dora alhakin tashin farashin dalar kan ’yan baranda da kan yaɗa bayanan da kan sa dalar ta cilla sama.

Sonubi ya ce, za su ɗau matakai da hakan zai jawo asara ga masu tada farashin dalar.

Da alamu Tinubu ya ɗau matakin ne bayan ’yan kwadago sun ƙara fitar da sabuwar matsaya kan matuƙar a ka sake cilla litar fetur sama, to za su afka yajin aikin da zai rufe dukkanin harkokin ƙasar.

Matsayar ta biyo bayan yiwuwar ƙara farashin litar fetur daga ƙungiyar dillalan man fetur IPMAN da ke cewa yadda dala ke cigaba da tashi zai iya tada farashin litar zuwa Naira 750 daga Naira 615.

IPMAN ta ce, ’yan kasuwa na samun dalar daga kasuwar bayan fage don akwai ɗawaniyar maida dala takarda daga canjin gwamnati.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC Komred Joe Ajaero ya ba da tabbacin afkawa yajin aikin sai yadda hali yayi matukar litar ta ƙara tashi.

Tuni kusan dukkan kayan masarufi su ka yi tashin gauron zaɓi inda talakawa da ma masu, matsakaicin samun kuɗin shiga ke cikin matuƙar damuwar rashin tabbas.

Fadar gwamnatin Nijeriya Aso Rock ta ce sam ba batun qara farashin man fetur a halin da a ke ciki ba kamar yadda a ke yaɗa raɗe-raɗin afkuwar hakan ba.

Kakakin shugaba Tinubu Ajuri Ngelale ya ruwaito shugaba Tinubu ya na ba da tabbacin ba za a ƙara farashin ba a yanzun nan don ma ga yadda a ka samu barazana daga ƙungiyar ‘yan ƙwadago.

Ngelale ya ce, ya samu damar zama su ka tattauna maganar da shugaba Tinubu inda ya nuna ma sa ba shirin ƙarin farashin.

Wanda ya saba da sanarwar ƙungiyar dillalan man fetur da ta nuna yiwuwar ƙarin farashin don yadda darajar Naira ke faɗuwa kan dalar da a ke shigo da man da ita.

Tun da gwamnati ta sake akalar farashin ga ‘yan kasuwa, yanzu sai a jira a ga me za ta yi wajen takawa ‘yan kasuwar birki.

Sabanin Nijeriya da ke cewa ba sake juyowa kan tallafin fetur duk da alwashin farashin ba zai ƙara cillawa ba ƙasar Kenya ta dawo da tallafin man fetur don yadda ’yan ƙasar su ka yi matuƙar fusata a sanadiyyar janye tallafin da hakan ya kawo matuƙar tsadar rayuwa.

Gwamnatin Kenya ta dawo da sashen tallafin don hakan ya kawo sauƙi ga farashin litar mai a kasuwa aƙalla a watan nan na Agusta zuwa watan gobe na Satumba.

Yanzu litar fetur za ta cigaba da zama kimanin dala 1.35 a Kenya bayan janye qarin dala 0.05.

A lokacin da ya hau karagar mulki a Satumbar bara, shugaban ƙasar William Ruto ya janye tallafin fetur da na fulawar masara da wanda ya gada ya sanya a zamanin mulkin sa.

Ruto ya ce, ya gwammace ya ba da tallafin samar da hajojin biyu ba wai yadda za a sayar da su a kasuwa ba.

Matakin Ruto ya jawo gagarumar zanga-zangar ƙin amincewa da matuƙar ƙuncin da al’ummar ƙasar su ka shiga.

Duk kuncin da za a shiga indai mutane na iya ba da shawara gwamnati ta saurara da sauƙi, amma duk lokacin da a ka samu gwamnati da kan cije kan wata matsaya ko da hakan ya sabawa buƙatun akasarin jama’a to akwai ƙalubale.

Dimokraɗiyya kan yi daɗi ne a lokacin da gwamnati kan zama mai sauraron ra’ayoyin jama’a da sharewa jama’ar hawaye ko da ta hanyar bayyana mu su hanyoyin da za a bi wajen kawo sauƙin rayuwa ne kuma a fara gwada wasu misalai na zahiri. Idan kuma a na kan wannan wahala sai a ka ga jami’an gwamnatin na bukukuwa da jigila cikin manyan motoci da jiragen sama, haƙiƙa hakan zai ɗorewa jama’a kai su kasa gane barcin makaho da farkawar sa.

In kasa na cikin damuwa to a gani daga yanayin yadda gwamnati ke aiyukan ta sese-sese ba sharholiya ba. Ai ba mamaki hakan ne ma ya sa ganin dan shugaba Tinubu wato Seyi ya na yawo da jami’an tsaro a Abuja ya na motsa jiki da takalmi mai taya ya zama abun magana har ma wani ya yi tsokana da cewa an shiga zamanin masu takalmin taya bayan kenan an gama zamanin masu hawa babur mai shegen gudu na ’yan jari hujja da nufin tuna yadda ɗan tsohon shugaban ƙasa Yusuf Buhari ya tava yin hatsari da irin waɗannan babura na garari.

Kammalawa;

Kawai kowa musamman tsakanin masu ƙaramin ƙarfi ya sauya tsarin rayuwa ya rungumi hanyoyi masu sauƙi a gare shi da aƙalla zai iya cin abincin da zai rayu. Magidanta su zauna da mutan gidan su, su ga yadda za su iya cin abinci duk rashin daɗinsa don su rayu. Masui ya magana kan ce in hagu ta kiya a koma dama. Babbar shawara a koma ga neman taimakon Allah da ya yi alƙawari ga masu bin dokokin sa cewa bayan tsanani akwai sauƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *