‘Ɓarayin Zamani: Babu shakka littafin makaranta ce mai zaman kanta
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
ɗanladi Z. Haruna ba ɓoyayye ba ne tsakanin marubutan adabi na Jihar Kano. Ya daɗe yana ba da gudunmawa a fannoni daban-daban, da suka haɗa da rubuce-rubuce kan ƙalubale da cigaban rayuwa, da ƙoƙarin ceto yanayin da kasuwancin littattafan Hausa ya shiga, da kuma hidimar zamanantar da harkar rubutun adabi. Duk da kasancewar ba duka matasan marubuta na onlayin ne suka san da gwagwarmayar da ya daɗe yana yi ba, saboda ƙarancin shekarun wasu a cikinsu. Amma shaidar baya-bayan nan da za a iya bayarwa game da gogewarsa a harkar rubutun adabi ita ce ta nasarar da ya samu a Gasar Rubutun Gajeren Labari ta Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano, inda ya zo a matsayi na biyu.
Na ci karo da littafinsa na ‘ɓarayin Zamani’, wanda ya shiga Gasar Tsangayar Gusau ta shekarar 2019 da shi, kuma ya yi nasarar zama na biyu. Littafin da ya fallasa yadda masu satar bayanai a zaurukan sada zumunta da sauran ɓangarori da fasahar zamani ta yanar gizo ta zo da su. Yadda suke damfarar mutane su sace masu kuɗaɗe a asusun su na banki, da yadda suke yaudarar masu son zuciya da sunan kasuwanci mai saurin kawo riba, ko yin kutse cikin wayoyin mutane suna aikawa da saƙonnin ƙarya don neman taimakon kuɗi da sauransu.
Lallai babu shakka wannan littafi makaranta ce mai zaman kanta, wacce mutum zai shiga domin neman ilimin yadda zai kare kansa, da yadda sanin dabaru da hikimomin da ɓatagari ke amfani da su suna zambatar jama’a maƙudan kuɗaɗe, da sanin irin manhajoji da kalmomin da waɗannan ɓarayin zamani ke amfani da su, don hana jami’an tsaro ko ƙwararru gano irin ɓarnar da suke yi, da hanyoyin da suke bi wajen ɓoye bayanai da kuɗaɗen da suke sacewa, ba tare da an gano su ba. Sai in har an dace da ƙwararrun gaske ko waɗanda suka taɓa bin irin wannan ɓarauniyar hanyar, kafin a iya cin lagon cutar da suke yi wa jama’a.
Littafin ‘ɓarayin Zamani’ da aka rubuta shi a shekarar 2014, amma sai a shekarar 2019 aka shiga Gasar Tsangayar Gusau inda ya yi nasarar zama na 2. Yana ɗauke ne da shafuka 269 da babi 22. Ya ba da labarin gungun wasu ɓarayin zaune ne da ke ɓata lokaci a yanar gizo ta hanyar amfani da kwamfiyutocin da suka mallaka, suna shiga manhajoji da wurare iri-iri cikin fasahar sadarwa da ake amfani da su yau da gobe, domin gano inda za su cutar da jama’a, su saci bayanansu, da dukiyoyinsu, waɗanda suka adana ba tare da cikakken tsaro ko kariyar da ta kamata ba. Waɗannan matasa da sakacin iyaye, rashin samun kammala karatu, da mugayen abokai suka jefa su a wannan mummunar harka sun samu nasarar yin kutse a manhajar wani kamfanin sayar da kayayyaki ta yanar gizo, inda suka haifar musu da tsaiko a kasuwancin da suke yi na fiye da tsawon awa 24, da ƙoƙarin durƙusar da kamfanin bakiɗaya. Kodayake, ba su samu nasarar cimma baƙar aniyarsu kan kamfanin ba, sakamakon gudunmawar da suka samu daga ƙwararrun jami’an tsaro da suka goge a harkar yaƙi da ɓarayin yanar gizo, da kuma wani ƙwararren matashi da ke aikin wucin gadi da kamfanin mai suna Mahmud. Daga bisani an samu nasarar ƙwato bayanan kamfanin da kuma gano inda ɓatagarin ke gudanar da mummunar harkar su tare da kama su, don su fuskanci shari’a.
A yayin da marubucin ɗanladi Haruna ke ƙoƙarin warware ƙullin da ya yi wa labarin mun karanta labarai iri-iri na yadda kowanne daga cikin waɗannan ɓarayi ya samu kansa a wannan gungu, da irin katoɓara da damfarar da ya yi a baya, har ya gudu ya samu mafaka a garin Kano, inda a nan marubucin ya gina labarin nasa. Sannan an ilimantar da mai karatu sosai game da ma’anonin kalmomin da ake amfani da su a fasahar zamani ta yanar gizo, ta yadda ko mutum bai je jami’a ko wata cibiyar ilimi ya karanci yadda ake sarrafa na’urar kwamfiyuta, gyaranta, da samar mata da kariya ta tsaro, don hana ɓatagari yi wa mai amfani da ita illa ba, zai fahimci dabarun da ake amfani da su da yadda zai yi wa kansa rigakafi.
Harwayau, akwai tarihin manyan ýandamfarar duniya, waɗanda suka fara ƙirkiro irin kasuwancin zamani da ake yi ta yanar gizo, inda ake yaudarar jama’a da sunan ruɓanya musu jarin da suka zuba cikin ƙanƙanin lokaci, don su yi arziƙi dare ɗaya. Mun karanta tarihin yadda rayuwar su duk ta ƙare a wulaƙance, duk da har yanzu wasu na nan na raya ayyukan su na damfara da cuta da suka zamanantar da su. Yayin da waɗanda suka yankawa kansu kazar wahala, da waɗanda son zuciya ya afka da su tarkon ýanshafimulera, da kuma waɗanda ƙaddara ta shafe su, suke faɗawa cikin komar waɗannan maha’intan mutane, masu zambatar jama’a.
Bayan ilimantarwa, harwayau littafin yana koyar da babban darasi da hannunka mai sanda ga masu mu’amala da shafukan sada zumunta, da kuma zaburar da jama’a su tashi tsaye su nemi ilimin fasahar zamani da yadda za su kare kansu daga ɓarayin zaune, masu amfani da jahilcin da jama’a ke da shi a wannan ɓangaren suna cutar da su.
Littafin ya yi gargaɗi ga mata masu fitar da hotunan tsiraici ko wani sashi na jikinsu a shafukan sada zumunta don birge maza da neman masoya, ko maza waɗanda ke ruɗuwa da ganin kyawawan hotunan ýammata suna biye musu da sunan soyayya a yanar gizo, wanda wani lokaci maza ne masu satar bayanai, da damfara. Ko kuma mutanen da suke bayyana sirrin su da na iyalansu a zaurukan sada zumunta, duk mun ga yadda suka gamu da mummunan sakamako.
Daga cikin abubuwan da suka burgeni da wannan littafi akwai kyakkyawan tsarin da aka gina labarin a kai wanda yake nuna ƙwarewa da gogewar marubucin. An yi amfani da daidaitacciyar Hausa, da kiyaye ƙa’idojin rubutu, da tsaftataccen harshe, wajen bayar da labarin. Sannan, marubucin ya yi ƙoƙari wajen fassara ma’anonin wasu kalmomi na kimiyya zuwa Hausa, yadda mai karatu zai yi sauƙin ganewa, duk kuwa da kasancewar kalmomi ne na kimiyya, kamar su ‘dandatsa’, ‘rariyar liƙau’, ‘saƙandami’, ‘ɗalamisai’, da sauransu. An kuma nuna muhimmancin tuntuɓar jami’an ýansanda, musamman waɗanda suka ƙware a wannan fanni, domin samun haɗin kansu wajen gano ɓarayin a duk inda suke da kuma daƙile cigaba da faruwar al’amarin ko datse tasirin da ɓarnar za ta jawo.
Kowanne mutum tara yake bai cika goma ba, kamar yadda masu hikimar magana ke faɗa. Duk da ƙoƙarin marubucin na kiyaye ƙa’idojin rubutu, akwai wasu wurare da aka samu tuntuɓen rubutu, da kuma wasu kalmomin da aka faɗe su a turanci saboda saurin a kammala rubutun, ko kuma ba a faɗe su a yadda suka dace ba. An yi amfani da da sunan Amerika a maimakon Amurka, da kiran sunan ƙasar London a maimakon birnin Landan, ko ƙasar Ingila, da makamantansu.
Muna sa ran ganin wasu rubuce-rubuce irin wannan masu ilimantarwa da nishaɗantarwa, daga marubuci Malam ɗanladi Zakariyya Haruna.
