Lokaci ya yi da makiyaya da manoma za su daina biye wa shaiɗan – Bala Dabo

Daga JOHN D.WADA LAFIYA

Jihar Nasarawa dai na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da a baya aka yi ta samun rigingimu tsakanin makiyaya da manoma. A yanzu da aka shiga daminar bana, Wakilin Blueprint Manhaja, John Wada Lafiya, ya samu tattauna da Shugaban Ƙungiyar nan ta Miyetti Allah Cattle Breeders ta ƙasa reshien Jihar Nassarawa, Alhaji Bala Mohammed Dabo, a ofishinsa da ke sakatariyar ƙungiyar a jihar. Tattaunawar ta kasance dangane da matakai da qungiyar ta ɗauka, don hana afkuwar rigirgimun tsakanin ɓangarorin biyu a bana. Ga dai yadda tattaunawar ya kasance:

MANHAJA: Rankayadade, damina ta sake zagayowa. Kuma a irin lokacin nan ba shakka akan samu rashin jituwa tsakanin makiyaya da abokan dabinsu manoma a jihar nan. A matsayinka na shugaba, ko za ka bayyana wasu matakai da kuka ɗauka don hana aukuwar lamarin a bana?
DABO: Da farko, na gode sosai da damar nan da ka bani don na bayyana wa duniya bakiɗaya wasu matakai ko dabaru da muka ɗauka don hana ɓarkewar rigirgimu tsakanin manoma da makiyaya a jihar nan. Ba shakka haƙƙi ne da ya rataya a wuyanmu mu yi iya ƙoƙarinmu wajen tabbatar da wanzuwar zaman Lafiya tsakanin al’ummomin biyu. Abu na farko da na yi kafin yanzu shi ne, na umurci dukka shugabannin ƙungiyarmu a duka ƙananan hukumomin jihar nan 13 da su tabbatar sun yi dukka mai yiwuwa wajen tabbatar da ba a samu tashin-tashinan tsakanin ɓangarorin biyu ba. A lokacin daminar nan kaɗai ba har bayan daminar. Yanzu wannan mutumin da ka ga ya bar ofishina nan kafin ka shigo, shugaban ƙungiyarmu ne na ƙaramar hukumar Awe. Shi ma na gayyato shi ne inda na umurce shi shi ma da ya tabbatar bana ba a fuskanci ƙalubalen rashin tsaron musamman tsakanin manoma da makiyaya dake yankin sa ba. Hakazalika, bayan wannan a yanzu shirye-shiryenmu ya yi nisa na wani babban taro da nake so na kira don mu tattauna yadda za a shawo kan rigimar bana. A yayin taron wanda muke sa ran za mu gudanar kwanan nan, za mu jawo hankulan al’umma ne bakiɗaya, musamman manoma da makiyaya dangane da buƙatar tabbatar da zaman Lafiya don idan babu zaman Lafiya, komai zai lalace. Wato noma da kiwon duk ba za a ci moriyarsu ba. Saboda haka, a taqaice waɗannan su ne kaɗan daga cikin matakai da muka ɗauka da waɗanda za mu kuma ɗauka nan gaba, don tabbatar da mun cimma wannan burin. Kuma ga duka alamu tuni haƙarmu ta soma cimma ruwa, don kawo yanzu bamu samu wani mumunar labari daga ɓangarorin biyu ba.

Ko da wata matsala da kuke fuskanta a kokarin nan da kuke yi na hana ɓarkewar rigimar tsakanin ɓangarorin biyu a bana?
Ba shakka kamar yadda ka sani a duk wani aikin cigaba da mutum ke yi, dole ne ya fuskanci wasu ƙalubalai. Tabbas muna fuskantarsu. Sai dai ina so na yi magana a kan manyan abubuwa guda biyu ne kacal, daga cikin waɗanda suka fi jawo mana tafiyar hawainiya a ƙoƙarin. Waɗannan abubuwa biyun su ne rashin abubuwan hawa da tallafi musamman na kuɗi. Ka ga ina so na sanar da kai cewa, a ƙungiyarmu mun kafa wani kwamitin matasa wanda suke gudanar da sintiri na musamman a yankunanmu don kamo ɓata-gari cikin mutanenmu. Ba shakka, matasan suna gudanar da ayukansu yadda ya kamata. Kuma kawo yanzu suna taimaka matuƙa wajen daƙile ayyukan ɓata-gari. Sai dai babban matsalar da muke fuskanta shi ne abubuwan hawa ga matasan don inganta wannan sintirin nasu. Idan a yau aka ce suna da mota da sauran abubuwa hawa ka ga da nasarori za su samu a aikin nasu da ya fi wanda suka samu a yanzu. Haka kuma batun tallafi, a gaskiya har yanzu ba ma samun tallafi musamman na kuɗi ga matasan. Ya kamata a yayin da suke gudanar da ayukansu na tabbatar da zaman lafiyar, idan ana tallafa musu da wasu kuɗaɗe ka ga su ma za su sa ƙwazo yadda ya dace. Saboda haka, akwai wasu ƙalubale da dama da muke fuskanta. Amma kamar yadda na bayyana, waɗannan su ne manyan. Haka su ma waɗannan shugabanninmu da nace maka suna isar da saƙonnin zaman Lafiya a yankunansu. Akwai wurare na nesa da ya kamata a ce an samar musu da tallafi da kuma abubuwan hawa don ba su damar isar da saƙonnin yadda yadace.

Ko ƙungiyar ku ta samu wasu nasarori ƙarƙashin shugabancinka kawo yanzu?
To, a gaskiya ba wai yabon kai ko wani abu makamancin haka ba. Kamar yadda ka sani ne tunda na zo a matsayin shugaban ƙungiyar nan tamu ta Miyetti Allah Cattle Breeders a jihar nan ba a fuskanci wani rigimar makiyaya da manoma ba. Wannan a bayyane yake za ka iya gudanar da bincikenka a matsayinka na ɗan jarida don ka tabbatar da haka. Ka ga hakan babbar nasara ce. Don kamar yadda na bayyana a baya, tunda na zo ban zauna ba. Ina kai komo ne wajen tabbatar batun rigimar manoma da makiyayan ya zama tarihi a jihar nan. Don na tabbata Allah da ya halicce mu ya kuma haɗa mu waje guda ya san dalilin yin haka. Kuma dole ne mu koyi haƙurin zama tare. Kuma da Allah ya tashi taimakona, sai ya sa duka ɓangarorin biyu wato manoma da makiyayan duk suna bani cikakken goyon baya har ma da sauran hukumomin tsaro a jihar nan. Duk suna yaba mana kuma muna aiki tare. Saboda haka, waɗannan su ma manyan nasarori ne. Akwai kuma zaman sulhu da dama da lokaci ba zai bari na bayyana maka dukka ba, da na yi ta yi. Kuma har yanzu ina yi tsakanin bangarorin biyu wanda ke taimakawa matuka wajen ɗorewar wanzuwar zaman lafiyar.

A ƙarshe, wanne saƙo kake da shi ga ‘ya’yan ƙungiyarku da manoman jihar nan bakiɗaya?
A kullum kiran da nake yi zuwa gare su shi ne, su ji tsoron Allahi dukkansu. Ka ga ɓarnar da makiyaya ke yi wa manoma kashi biyu ce. Ka ga na farko, akwai ɓarnar ganganci sannan akwai kuma ɓarnar kuskure. Idan Fulani ya yi maka varna da gangan, abinda muke cewa a kullum shi ne, a kawo ƙarar su. Kuma a matsayinmu na shugabanni, mun san hukuncin da ya dace mu ɗauka a kansu, kuma a biya manomin hakinsa, idan bai yafe ba. Haka kuma idan makiyayi ya yi maka ɓarna da kuskure, to sai ka duba ka ga ko za ka iya yafe masa. Idan kuma ba za ka yafe ba, don Allah kada ka dauki doka a hannun ka. Maimakon haka, ka tuntuɓi hukumomin da suka dace su bi maka haƙƙinka, bayan an tabbatar da laifin makiyayan. Mu kuma a namu ɓangaren, mu tabbatar an yi maka adalci. Amma sau da yawa abinda ke jawo tashin-tashinan shi ne, batun ɗaukar doka a hannu. Inda za ka ga manomi ya ce shi zai rama ɓarnar da aka yi masa nan take, ko a jikin dabbar ko mai kiwon, ko kuma a sa wa dabbar guba ta ci, ta mutu. Ka ga za a iya fuskantar matsala sakamakon haka. Saboda haka, ina so na yi amfani da damar nan na nanata kira na zuwa ga ɓangarorin biyu cewa don Allah a ji tsoron Allah, a riwa kare haƙƙin juna. Mu a ɓangarenmu na shugabanni kamar yadda na bayyana a baya, tuni mun riga mun qudiri aniyar tabbatar da ɗorewar zaman Lafiya da ake mora a yanzu a jihar nan. Amma ina mai tabbatar maka cewa lallai hakan ba zai yiwu ba muddin dukan mu ba mu koyi haƙuri da juna ba. Lokaci ya yi da yakamata mu yi la’akari da abubuwa da sheɗan ke yin amfani da su wajen jawo mana rashin jituwa mu kuma riƙa ƙaurace musu. 

Na gode sosai.
Mu ma mun gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *