Lokaci ya yi da ya kamata mata su zama jagaba a al’amuran ƙasa-Honorabul Habiba Balarabe

“Don samun damar ci gaba da agaza wa al’umma ne na shiga siyasa”

Honorabul Habiba Balarabe Liman, gogaggiyar ‘yar siyasa a Jihar Nasarawa da ƙasa bakiɗaya. Ta taɓa fitowa takarar kujerar mamba mai wakiltar mazaɓar Keffi da Kokona da Karu a Majalisar Wakilai ta Tarayya. A yanzu ita ce mataimakiyar gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ta musamman. A zantawarta da wakilinmu, ta bayyana tarihin rayuwanta, inda ta kuma buƙaci ‘yan’uwanta mata a jihar da ƙasa bakiɗaya su yi amfani da yawansu wajen ƙwato ‘yancinsu da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Daga JOHN D. WADA, Lafiya

MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki a taƙaice.
HONORABUL HABIBA: Da farko sunana Honorabul Habiba Balarabe Liman. Ni asalin ‘yar jihar nan ce, daga Ƙaramar Hukumar Keffi. An haife ni a garin Jos, Jihar Filato, a shekarar 1975. Na yi karatu nursery da firamare ɗina a nan garin Jos, inda na kammala a Abuja. Daga nan na ci gaba da karatuna a Kwalejin mata zalla na tarayya da ke Gwarinpa a Abuja. Na ci gaba da karatu a babbar jami’ar Abuja inda bayan na kammala na yi hidimar ƙasa ɗina a jami’ar. Ni ce ‘ya ta farko a gun iyayena. Ka ji kaɗan daga cikin tarihin rayuwata kenan.

ko akwai ƙalubalen da kika fuskanta na tasowa?
To ni dai a gaskiya ba wai fariya ba, ko wani abu makamancin haka ba. Zance alhamdulillah ban fuskanci ƙalubale masu yawa ba a rayuwata da nake tasowa. Domin iyayena sun yi iya ƙowarinsu wajen tabbatar ban fuskanci ƙulabale a rayuwata ba da nake tasowa. Sun nuna min so da ƙauna sosai. Abu guda ɗaya kacal dazan iya cewa na fuskanta a matsayin ƙalubale shine yadda mahaifina yakasance mutum ne da baya barin al’adu ko wani abu makamancin haka ya shafi harkokinmu. Ina nufin mutum ne da yakan bamu dama mu bi ra’ayinmu muddin ra’ayin bai saɓa da tarbiyya da aƙidarsa a gare mu ba. Yakan ƙarfafa mu, mu riƙa fito fili muna bayyana ra’ayinmu da babbar murya. A lokacin nakan yi gaban sauran sa’o’ina amma sai yakai ga dole na riƙa tafiya a hankali don kasancewa daidai dasu kamar yadda al’ada ya tanadar da sauransu. Saboda haka wannan a wurina wani ƙalubale ne dana fuskanta a lokacin. Bayan wannan a gaskiya ban fuskanci ƙalubale da nake tasowa ba da hakan a gaskiya ya bani damar tsara yadda rayuwana zai kasance. Kuma bazan taɓa manta wa da wannan sadaukarwa da iyayena sunyi mini ba. Ina fatan Allah ya saka musu da alheri.

Mene ne burinki a lokacin da kike tasowa?
Akwai abubuwa da dama da na so in zama da na ke tasowa. Amma babba daga cikinsu wanda zan tuna a koyaushe shi ne, na so in zama mai shirin fim ce. Bayan wannan na kuma kasance da burin zama mai rawa. Na kuma so in zama matuƙiyar jirgin sama. Har ila yau ina kuma so in zama lauya da dai sauransu. Amma ga shi a yau da ikon Allah sai na kasance ‘yar siyasa mai taimaka wa maigirma gwamnan jihar nan Injiniya Abdullahi Sule na musamman. A taƙaice dai a yau zaka iya kira na ‘yar siyasa.

Ko akwai wani abu da kike so wata rana a tuna ki da shi?
A gaskiya zanso a tuna dani a matsayin wacce ta sadaukar da komai wajen bauta wa al’umma bakiɗaya musamman marasa galihu. Inaso a tuna dani a matsayin wacce ta kawo canji mai ma’ana a rayuwar al’umma bakiɗaya. Don kamar yadda ka sani a yanzu akwai munanan ɗabi’u da dama da suke jawo matsaloli a rayuwar al’ummarmu. Shiyasa a kullum muna ƙoƙarin kawo canji a rayuwarsu don sa su a tafarki da ya dace. Saboda haka a taƙaice kamar yadda na bayyana zan so a tuna da ni a matsayin wacce ta bauta wa al’umma a fannoni da dama don kawo canji mai ma’ana a rayuwansu a kullum.

Me ya sa ki sha’awar shiga siyasa?
Wato abinda ya ba ni sha’awa ko ince ya jawo ra’ayina a harkar siyasa shi ne, kasancewa ina da wata gidauniya da ake kira Fatima Zara Foundation inda na ɗauke sama da shekaru 11 ina taimaka wa mabuƙata da sauran jama’a bakiɗaya. Hakan ya sa a kullum ina tare da jama’a. Kuma a hankali sai naga ya dace in shiga harkar siyasa don in samu cikakken damar ci gaba da agaza wa al’umma ta. Na fahimci cewa idan ina siyasa zan samu damar ci gaba da bada cikakken gudunmawa ta wajen kawo canji a rayuwansu. Kuma da yardar Allah abinda na ke yi kenan. Wato ina iya ƙoƙarina dai dai gwargwado wajen tallafa wa al’umma musamman marasa galihu da naƙasassu da sauransu. Shiyasa ka ga mai girma gwamnan jihar nan Injiniya Abdullahi Sule ya ƙirƙiro da wannan ofishi da ke kula da harkokin jin daɗin al’umma bakiɗaya don suma su san ana yi da su.


Saboda haka a taƙaice dai zance na shiga harkar siyasa ce don in ci gaba da jawo ayukan cigaba wa al’ummata da sauransu. Kuma na lura kafin ka iya cimma wannan buri dole ne ka kasance mai magana da babbar murya a matsayinka na mai magana da yawunsu. Kodashike da farko ban taɓa yin tunanin shiga harkar dumu-dumu ba, amma daga baya na ga ya dace inyi haka saboda al’ummata.

Wace shawara za ki ba wa ‘yan’uwanki mata?
Wato da farko wani abu da na lura shi ne, lokaci ya riga ya wuce da ‘ya mace ke kasancewa a baya a dukka fannonin rayuwa. Kamar yadda ka sani mu mata muna da yawa ba a jihar nan kaɗai ba, har da ƙasa bakiɗaya. Saboda haka idan za mu haɗa kai mu yi amfani da wannan ƙarfinmu, ba shakka za mu iya ƙwato ‘yancinmu a dukka fannonin rayuwa. Kusan komai yanzu ana yin la’akari da yawan mutane ne kuma mu mata muna da yawan. Kuma a duk inda ka tafi za ka tarar mata ne suka fi yawa. Shiyasa a kullum na ke kira a gare su cewa, lokaci ya yi da mu mata yakamata mu kasance jagaba a al’amuran jihar nan da ƙasa bakiɗaya. Dole mu riƙa ƙarfafa junanmu mu kuma riƙa haɗa kai don cimma wannan buri. Kuma dole ne mu tarbiyyantar da al’umma bakiɗaya dangane da munanan ɗabi’u dake daƙile ayukan ci gaba a ƙasar nan bakiɗaya a matsayinmu na iyayen ƙasa bakiɗaya. Ka ji shawara da nake da shi kenan agaresu a taƙaice.

Ko za mu iya sanin nasarorin da sabuwar gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta cimma kawo yanzu?
A gaskiya zance da babbar murya cewa kawo yanzu gwamnatin maigirma Injiniya Abdullahi Sule kawo yanzu ta samar wa ɗimbin al’ummar jihar nan da ribobin dimokaraɗiyya ta kyawawan shirye-shirye da manufofinta da take ƙirƙiro. Idan ka zagaya za ka iya gane wa idanunka waɗannan ayukan cigaba da yake aiwatar a kullum. Saboda haka gwamnan yazo ne da kyawawan shirye-shirye, kuma yana aiwatar da su. Al’ummar jihar nan kuma suna amfana da su matuƙa.

Mun gode ƙwarai.
Ni ma na gode.