Lokaci ya yi ga Zalenskyy ya miƙa wuya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk mai kula da yanda lamuran siyasar duniya ke tafiya musamman kan yaƙin mamayar Yukrain da Rasha ta ke yi zai iya hasahen lokaci ya yi ga shugaban Yukrain Volodymyr Zelenskyy ya miƙa wuya don samun sulhu da dakatar da kai hare-hare. Dama Zelenskyy ya na tinƙaho ne da neman shigar sa ƙungiyar tsaro ƙasashen yamma wato NATO don haka ya ke ganin zai iya fito na fito da Rasha. Mu sani cewa dama Yukrain sashen babbar Dualar taraiyar Sobiyet ne ko ma a ce yankin Rasha ne. Samun ‘yancin ƙasashen Sobiyet daban-daban bai hana Rasha zama babbar Dualar da ke faɗa a ji a duniya ba. Neman kaucewa tasirin Rasha da haɗa kai da ƙasashen yamma da ke hamaiya da muradun Rasha da Zelenskyy ya yi, ya sanya shugaban Rasha Vladimir Putin ɗaukar matakan kwance ɗamarar yaƙin Yukrain amma ba da niyyar wargaza ƙasar ba. Hakika inda Rasha na da zummar yaƙin a yi ta ta kare ne da tuni ta gama da Yukrain. A lokacin da wannan bijirewa ta auku ƙasashen yamma sun ɗau matakin marawa Yukrain baya da ba ta makamai da kuma aza takunkumi ta vangarori daban-daban don karya tattalin arzikin Rasha. Gaskiya Rasha ta jajirce ta ki yarda ta yi ƙasa a gwiwa kuma ta dau matakan kauda bara wajen juya hulɗar ta zuwa ga wasu ƙasashen ga lamuran diflomasiyya da cinikaiya. A hakan Rasha ta ƙarfafa wata ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen duniya mai taken BRICS da ta haɗa da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afurka ta kudu.

Wasu ƙasashen ma sun nuna sha’awar shiga wannan tafiya da ke da zummar samar da alƙibla da za ta yi gogaiya da babakeren ƙasashen yamma kan tattalin arzikin duniya. Kazalika BRICS na son kawo ƙarshen tasirin Dalar Amurka a hada-hadar kuɗi ta duniya. ƙarar da a ka kai shugaba Putin ga kotun duniya kan laifukan yaƙi a Yukrain ga kotun duniya bai yi gagarumin tasiri ba. Kotun dai na son a kamo Putin don gurfanar da shi gaban ta amma dama manyan shugabanni irin waɗannan ba su tava faɗawa komar kotun ba. Rasha ma cewa ta yi ba ta ma cikin kotun don haka hukuncin kotun bai ma shafeta ba. Zelenskyy dai bai samu abun da ya ke so na ƙasashen NATO su shigo a fafata da su don wargaza Rasha don ba shakka hakan zai iya kawo gagarumar asarar rayuka da dukiya da zai iya zama tamkar yaƙin duniya na uku. Haƙiƙa duniya ba ta buƙatar wani yaƙi na gama gari tun bayan yaƙin duniya na biyu inda ya zama an shiga yaƙin cacar baki ko tsama tsakanin Rasha, Sin da ƙasashen yamma. Don haka Amurka a lokacin tsohon shugaba Joe Biden ta tallafawa Yukrain da makamai. ƙasashen Turai ma irin Jamus sun tura tallafin makamai ga Yukrain ɗin. Gaskiyar magana hakan da NATO ta yi ya fi zama maslaha da afkawa yakin kai tsaye don zai iya jawo amfani da makaman kare dangi da duniya sam ba ta buƙatar hakan. Rasha kan kai hare-hare wasu sassa na babban birnin Yukrain wato Kyiv da wasu yankunan ƙasar don rage ƙarfin soja da makamashi. Hakanan Yukrain ɗin ma na kai hari cikin Rasha har ta taba ruguza wata gada mai muhimmanci. Dole tattalin arzikin Yukrain ya tabu domin in ka ɗebe wata yarjejeniya inda Turkiyya ke daukar nauyin jigilar hatsin Yukrain zuwa kasuwa hakan ya tsayar da lamuran Yukrain don hatta ita kan ta yarjejeniyar sai da amincewar Rasha. A nan wace riba turai da Amurka za su cimma daga yakin?. 

A zahiri indai ribar wasu ƙasashe da ke makwabtaka da Rasha su zama membobin NATO ne da kamar wuya kuma in hakan na nufin amfani da makwabtan Rasha don wargaza Rasha ne to me zai biyo baya in ya wuce sake haifar da ƙasar da sai an cigaba da taimaka ma ta da abun masarufi da kuma sunan kafa dimokraɗiyya. Kuma ko hakan ma nauyin na kan Amurka ne. Kazalika hakan ma mafarki ne don yaƙi ne da za a iya yin haihuwar guzuma da kwance uwa kwance don haka ina amfanin baɗi ba rai. Wannan a zahiri ya sa NATO ta shiga yaƙin ta bayan fage don kar ya juye yaƙi tsakanin Rasha da yammancin duniya ko ƙasashen gabashi da yammaci. Mun  tuna yanda gwamnatin Putin ta ɗau mataki kan shugaban rundunar ta ta sojan haya WAGNER wato Yevgeni Prigozhin wanda ya tabka kuskuren kushe ƙasarsa kan yaƙin da ta ke yi da Yukrain inda har ya nuna tamkar yakin ma bata lokaci ne. Ba ma sai an faɗa ba wannan matsaya cin amanar kasa ne ga mutum mai muhimmanci irin Prigozhin da ke jagorantar gagarumar rundunar da Rasha ke tinkaho da ita wajen tura daukin soji a sassan duniya. Wata dabara ta gwamnatin Putin ita ce ta nuna an yafewa Prigozhin ko kuma a ce ba a ɗau matsayar sa a matsayin wani laifi ba don shi din ya na da ’yancin fadar albarkacin bakin sa.

Prigozhin ya dawo gida a ka karrama shi da tarba ta musamman inda a lokacin da ya shiga wani jirgi sai ya samu hatsari kuma shi da muƙarrabai su ka rasa ran su. Masu sharhi sun tabbatar da zargin cewa Putin ne ya shiryawa Prigozhin gadar zare don hukunta shi a sanadiyyar cin amanar Rasha da ya yi. Kun ga a nan Rasha ta kare kasar ta ne daga kutse na abokan hamaiya a duniya da ya kai za ta iya ɗaukar ko wane mataki wajen kawar da mai kawo cikas ga yaƙin Yukrain gabanin cimma muradin yaƙin. Duk wani sojan Rasha da ya rasa rai a artabun Yukrain kan zama gwarzo mai kishin kare ƙarfi da ’yancin Rasha. Putin dai ya zama shugaban Rasha mai dogon zamani don yanda ya ke jan ragamar ƙasar da yin nasarar kare muradun ta a duniya. Har dai da a ce Putin ɗan Lakada-ka-was ne da tuni an gama da shi amma ya na cigaba da jan zaren sa. Putin ya yi zamani da shugabannin NATO daban-daban kuma sun gushe sun bar shi a fadar Kremlin. Haƙiƙa dawowar shugaba Donald Trump fadar White House da irin manufofin san a kin jini kashe dukiyar Amurka  ga mara baya ga yaƙe-yaƙe a sassan duniya, ya isa sako mai ƙarfi ga Zelensky ya fara tunanin shafawa kan sa ruwa.

Amurka ta caccaki Yukrain da nuna taurin kai wajen neman sulhu don dakatar da yaƙi da Rasha.

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya fara nuna damuwar Amurka ga shugaban Yukrain Volodymyr Zelenskyy a ziyarar aiki da ya kai fadar White House.

Vance ya zayyana Zelenskyy da shigowa har fadar White House ya na furta kalaman na rashin girmamawa ko rashin ɗa’a.

Zelenskyy ya nuna ai tun 2014 Rasha ta mamaye Yukrian da kawo matakai masu tsauri ta hanyar kuma sava yarjejeniyar da a ka ƙulla.

Kazalika kan yarjejeniyar amfana da ma’adinan Yukrain da Amurka ke kullawa, Zelenskyy ya ce hakan sai dai ya zo da tabbacin ba wa Yukrain tsaro.

Shugaba Trump da kan sa ya shiga maganar inda ya nuna matuƙar Zelenskyy bai amince da batun sulhu da Rsaha ba, Amurka za ta janye gaba ɗaya daga tallafawa Yukrain ɗin wanda ita ma ta san matsalar da za ta shiga.

Da alamu Zelenskyy na nuna fushi ne da taron da Amurka ta yi da Rasha a Riyadh ɗin Saudiyya ba tare da gayyatar Yukrain din ba.

Taron dai da wakilan Amurka da Rasha su ka gudanar a Riyadh ta haska manufar murka ta kawo ƙarshen yaƙin Yukrain da aiki tare da Rasha maimakon cigaba da zaman doya da manja. Fadar Kremlin ta yaba da taron da nuna nasara ce a ka samu. Rashin gaiyatar ƙasashen turai da ma ita kan ta Yukrain na nuna manyan ƙasashen biyu na son ɗaukar matakin kawo ya tsaya a hurumin sa don samun salama da jan akalar sauran ƙasashe kan lamuran tsaro ta hanyar da ba za a rika samun cin karo da juna ga muradu bisa manufa ba. Kuma an san cewa Amurka ke kan gaba a lamuran NATO ko ma a ce ita ce jigo a wannan ƙungiyar tsaron da kashe makudan kuɗi. Juyawa Zelenskyy baya da Amurka ta yi ya nunawa Zelenskyy alamu ƙarara na lokaci ya yi da zai sauya dabara. Shi kan sa ma ya furta har dai za a samu salama zai iya sauka daga mukamin sa. Duk fadan da ba riba ai barin sa ya fi alheri. Mun san cewa yaƙin Yukrain ya rutsa da ɗaliban ƙetare da ke karatu a can inda ya zama wajibi a kwashe su daga ƙasar a dawo da su ƙasashen makwabta zuwa maida su ƙasashen su na asali.

Kammalawa;

Bayan arangamar Zelenskyy da shugaba Trump a fadar White House, ya samu mara baya daga ƙasashen Turai da ke nuna su na tare da shi. A fili ya nuna dukkan ƙasashen turai na gefe guda Amurka na daya gefen! Shin Zelenskyy zai biyewa mara baya ta fatar baki daga Turai ya cijewa muradun Amurka? Gaskiyar magana gara gidadanci da ganganci.