Lokacin Hunturu: Matakan da suka wajaba a ɗauka don zama lafiya

A duk lokacin da aka shiga hunturu, wato lokacin sanyi da iska, wani lokaci ne da yanayi kan canja, wanda kowa da irin yadda yanayin yake zuwa masa, ta yadda wasu sukan samu kansu cikin wani yanayi na ƙunci, wasu kuma a wannan lokaci ne suka fi samun jin daɗin yanayi ta rayuwarsu gaba ɗayanta.

Lokacin hunturu, lokaci ne na tsananin sanyi, iska da kuma ƙura, kuma wannan yanki namu na Arewa ne abin ya fi tsanani, ta yadda wasu lokuta ma hatta yanayin samaniya kan canja, a kan yi hadarin sanyi kamar yadda ake yin hadarin ruwan sama. Lokacin yakan fara gadan-gadan ne daga watan Disamba zuwa Janairu.

Wannan lokaci, masana harkar lafiya su kan yi ta bayanai na jan kunne, musamman ga yara ƙanana da tsofaffi da suka manyanta, ta yadda za su rinƙa kula da yanayin jikinsu don kauce wa faɗawa cikin yanayi na rashin lafiya, musamman mura da irin zazzaɓin nan da yanayin kan jawo.

Baya ga waɗannan abubuwa kuma, akwai wani abu mai haɗari da wannan yanayi kan zo da shi, wato na iska mai ƙarfi, wanda idan ba kula aka yi ba, wannan yanayi kan jawo a rinƙa tafka gobara a gidaje, dazuka da kasuwanni. Wanda idan wannan yanayi ya zo, mahukunta kan fito su yi ta gargaɗi game da barin yara na wasa da wuta, ko barin wuta haka nan ba tare da ana kula da ita ba.

Wannan yanayi idan ya zo yana zuwa da iska, don haka sai ya zama idan ba hankali aka yi ba, ana yawan samun munanan gobara a wurare da dama, inda ake tafka munanan asarori a sanadiyyar gobara.

Idan muka koma ta fannin kiwon lafiya, masana a harkar suna yawan yin kira da jan hankali game da ɗaukar wasu matakai don ganin ba a faɗa a cikin wani mawiyacin halin da lokacin kan haddasa ba. Musamman kamar mura mai tsatsani, farfashewar jiki, tun daga baki, fata har ƙafafu, tari da sauransu. Sannan kuma akwai yanayin da mutum zai ji ƙasusuwansa na ciwo.

Zamanin hunturu, lokaci ne da ya kamata a ce jama’a na kula da duk harkokin da suka shafi lafiya da dukiyarsu domin kauce wa duk wani abu da za a ce an yi sakaci, musamman idan aka yi irin kiraye-kirayen da masana ke yi idan wannan lokaci ya shigo.

Masana harkar lafiya, kamar yadda na faɗa a sama, suna jan hankali, tare da bayar da shawarwari game da yadda za a tunkari wanann yanayi, da kuma yadda za a yi a lokacin da ya shigo gadan-gadan.

Wani Likiti, wanda ya bayyana sunansa da Dk. Femi, ya bayar da shawarar cewa akwai muhimmanci ga mutum in zai kwanta ya zama ya kwanta cikin bargo, ko wani mayafi da zai rufe masa jikinsa don kauce wa jin sanyi, da yadda zai samu kariya daga cututtukan da ake ɗauka ta hanyar shigar sanyi jikin mutum.

Likitan ya ci gaba da bayyana cewa masu ɗauke da cututtukan Asma da masu Sikila, su ne suka fi jin jiki a wannan lokaci. Don haka ya yi kira gare su da su kasance cikin kariya daga yanayin da zai sa su fita cikin sanyi ko shaƙar iskar da yanayin ke da ita. Domin wannan yanayin yana ƙara ba da dama ga cutar da ke tashi daga ƙashi, yana ƙara jawo kamuwa da cutar.

Haka kuma binciken da na gabatar ya tabbatar da cewa irin sanyi da iskar da wannan lokaci ke ɗauke da su suna taimaka wa wajen yaɗa cututtuka, wanda hakan ta sa ake yawan samun tashin cututtukan zamani, musamman ga masu ɗauke da cutukan da muka ambata a sama, wato Asma da Sikila.

Don haka akwai matuƙar muhimmanci ga jama’a, musamman masu ɗauke da cututtukan da muka ambata a sama, su kula da yanayin tufafin da za su rinƙa sanyawa a wannan lokaci na hunturu, su kasance masu rufe jikinsu ta kowane hali.

Haka kuma game da tsagewar jiki, akwai matuƙar muhimmanci a rinƙa shafa mai, wanda zai taimaka wajen jiki ya kasance cikin maiƙo, ba wai a bushe ba, domin bushewar jikin ne zai sanya shi ya tsattsage.

Wani abu mai muhimmanci, kamar yadda masana harkar lafiya suka bayyana, shi ne wajen cin abinci, ya kasance ana cin abinci mai zafi, ko mai ɗumi, a kiyaye cin abinci mai sanyi, domin cin abinci mai zafi zai hana ƙwayoyin cuta samun wurin zama.

Sannan akwai matuƙar muhimmanci a riƙa yawaita shan ruwa a wannan lokaci, domin jiki na buƙatar ruwa a lokacin.