Lookman ya shiga cikin takarar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana

ɗan wasan Nijeriya, Ademola Lookman yana gaba a jerin ’yan takara biyar a ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afirka na bana.

Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka, CAF ce ta bayyana sunayen ’yan wasan ranar Litinin da ake sa ran fayyace gwarzon bana.

Lookman ya ci ƙwallo uku a wasan ƙarshe a Europa League da ta kai Atalanta ta lashe kofin, sannan ya taka rawar gani da Super Eagles ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a baɗi.

Yana takara tare da ɗan ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, wanda ya lashe Ligue 1 a Paris St Germain da ɗan ƙasar Guinea, Serhou Guirassy, wanda ya ci ƙwallo 28 a Bundesliga a kakar da ta wuce a Stuttgard, hakan ya sa Borussia Dortmund ta saye shi.

Sauran sun haɗa da Simon Adinga mai taka leda a Brighton & Hoɓe Albion, wanda ya buga gasar da Iɓory Coast ta lashe kofin Afirka da mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Ronwen Williams.

Koci-kocin tawaga 54, waɗanda suke mamba a hukumar ƙwallon ƙafar Afirka ke yin zaɓen tare da wasu ƙwararrun.

Ana sa ran bayyana gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afirka na bana ranar 16 ga watan Disamba a birnin Marrakech a Morocco.