MƊD da Ukraine sun buƙaci tsawaita yarjejeniyar da aka ƙulla da Rasha

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres sun yi kira da a tsawaita yarjejeniyar da aka ƙulla da gwamnatin Moscow wadda ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi ta tashar ruwan tekun Black Sea.

Shugaban na Ukraine ya jadaddawa Guterres a birnin Kyiv cewa shirin samar da hatsin yana da matuƙar muhimmanci ga duniya, da kuma sassauta farashin abinci a duniya.

Yarjejeniyar ta kwanaki 120 da Majalisar Ɗinkin Duniya da Turkiyya suka ƙulla tun a watan Yulin da ya gabata kuma aka tsawaita a watan Nuwamba, za a sabunta ta ne a ranar 18 ga Maris idan har babu ɓangaren da ya nuna adawa da hakan.

Majiyar diflomasiyyar Turkiyya ta ce, har yanzu ba a biya buƙatun Rasha ba, inda ta ƙara da cewa gwamnatin Ankara na aiki tuƙuru don ganin an ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Manyan ƙasashen yammacin duniya sun ƙaƙaba wa Ƙasar Rasha takunkumi mai tsauri kan mamayar da ta yi wa makwabciyarta Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun bara.

Yayin da kayayyakin abinci da taki da Rasha ke fitarwa zuwa ƙasashen waje ba za su fuskanci takunkumi ba, Moscow ta ce takunkumin da aka sanya mata na biyan kuɗaɗenta, da kuma masana’antar inshora shinge ne ga jigilar kayayyaki.

Ukraine da Rasha na kan gava wajen samar da hatsi da taki a duniya.

Kafin Rasha ta auka mata, Ƙasar Ukraine ta kasance ƙasa ta huɗu wajen fitar da masara a duniya kuma ta biyar a jerin masu sayar da alkama, babbar mai samar da kayayyaki ga ƙasashe matalauta na Afirka da Gabas ta Tsakiya waɗanda suka dogara da shigo da hatsi.