Maɗaba’ar Kano ta samu kayan aiki da za ta zama ta ɗaya a Arewa – DMD Adamu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Maɗaba’ar Gwamnatin Kano KPPC mai buga muhimman takardun sirrin gwanati da sauran takardun amfanin al’umma da wallafe-wallafe na gwamnati da na kamfanoni da sauran al’umma yanzu haka ta farfaɗo da ga dogon suman da ta yi na rashin aikin yi da rashin kayan aiki wanda yanzu ta samu kayan aikin da za ta iya zama ta ɗaya Arewacin Nijeriya kamar yadda Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake son ganinta, wanda hakan ce tasa daga zuwansa ya ba su  dama da busa mata rai ta farfaɗo ta hanyar bada damar a cewa dukka abinda muke so mu faɗa za a yi kuma shi mai faɗa da cikawa ne kuma haka aka yi wanda wannan damar da muka samu da ga gwamna da Allah ya yardar masa ta sa babu abunda za mu ce sai dai cigaba da Godiya ga Allah da shi Gwamnan Kano.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin DMD Adamu Yahaya mataimakin Shugaban hukumar maɗaba’ar Gwamnatin Kano da ake kira da Kano Print Press Company, KPPC a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin MD Yahaya M Idris a wannan makon da ya gabata a harabar hukumar da ke birnin Kano.

Har ila yau ya ce maɗaba’ar ta gwamnatin Kano mai sassa daban-daban domin tabbatar da ingancin aiki da kuma tsare-tsare na yadda  maɗaba’ar take tafiyar da aikinta akwai sashi na buga takardun sirri da sauran takardu masu daraja wanda suka zo suka samu injina biyar amma ɗaya ne ke aiki zuwansu aka gyara su gaba ɗaya kuma aka ƙaro ɗaya yanzu dukkaninsu suna aiki.

“Sai kuma sashin samar da takardu da makamantansu; akwai injina uku dukkaninsu ba sa aiki, sashin ma ya kasance ma’aikatan sai dai su yi bacci amman zuwanmu an gyara injina uku kuma an samu qarin uku kamar yadda ya kamata.
“Haka sashin kwamfuta da uku ne kacal KPPC amma akwai kwamfuta guda takwas rigis suna aiki, kuma wani qarin ci gaban da aka samu a wannan maɗaba’a shine yanzu haka akwai maganar gina cibiya domin horar da matasa wannan sana’a wanda har gwamna ya bada kwngilar aikin kuma wannan na daga cikin dalilai dake KPPC za ta ma takwarorinta fintinkau Arewa.

A ƙarshe ya yabawa Gwamnan Kano da shugaban Maɗaba’ar kan kishin Maɗaba’ar da cigabanta da sauran maaikatanta inda yayi kira ga maaikatin Gwamnatin Kano da subi umarnin na kawowa ma’aikatar duk wani aiki na ɗab’i da suke buƙata haka kuma ya shawarci kamfanoni da sauran yan kasuwa ga al,uumar Kano masu kisshin Kano da su haɗa kai da wannan maaikata akan aikace-aikacen aikinta na ɗab’i da ta yi nisa wajen tsare-tsare na ziyartar su wuri-wuri har da jihohi Nijeriya domin yin aiki domin aiki dare da rana akan duk wani abu da suke buƙata a KPPC.