Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa sun sha rantsuwar kare sirri

Daga UMAR M. GOMBE

Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Tijjani Umar, ya gargaɗi ma’aikatan Fadar kan cewa bayyana wa duniya bayanan sirrin Fadar Shugaban Ƙasa ba tare da izinin hukuma ba laifi ne babba wanda ke tattare da hukunci ga duk wanda aka kama ya aikata hakan kamar yadda yake ƙunshe cikin dokokin aikin gwamnati.

Umar ya wannan gargaɗi ne a lokacin da yake rantsar da ma’aikata masu kula da muhimman bayanai a Fadar Shugaban Ƙasa a Talatar da ta gabata.

Ya ce, “Sakamakon sauya wa jami’ai wurin aiki da kuma murabus da wasunsu suka yi, ya sa muka ɗauki matakin maye gurabensu saboda muhimmancin ayyukan da suke yi.”

Ya ci gaba da cewa, “Wannan ne ma ya sa aka naƙalta wa ma’aikatan rantsuwar riƙe sirrin gwamnati tare da faɗakar da su muhimmancin bayanan da za su riƙa kulawa da kuma illa da sakamakon da ke tattare da fallasa bayanan.”

Umar ya ce kawo yanzu ba su fuskanci wata matsalar saɓa wa dokar aiki ba kuma ba su sa ran faruwar hakan.

Ya ce haƙƙi ne a kansu su sanar da ma’aikatan dokokin aiki ta yadda duk wanda aka samu ya saɓa ƙa’ida, idan bincike ya tabbatar da ya aikata laifin babu shakka doka za ta yi aikinta.

Yayin da ma’aikatan ke shan rantsuwa

Tun farko sa’ilin da yake bayani gabanin rantsar da ma’aikatan, Daraktan Sashen Ayyuka na Musamman na ofishin Sakataren Gwamnantin Tarayya, Tukur Yahaya, sai da ya yi wa ma’aikatan tambihi kan Dokar Kiyaye Bayanan Sirrin Gwamnati ta 1962.

Tare da cewa, akan rantsar da ma’aikatan ne domin tabbatar da killace bayanan sirri na gwamnati da kuma harkokinta.