Ma’aikatan lafiya 400,000 sun yi kaɗan a Nijeriya, inji minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Ali Pate, ya ce ma’aikatan kiwon lafiya 400,000 a Nijeriya ba su isa ba wajen biyan buƙatun kiwon lafiyar ‘yan Nijeriya.

Pate ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, bayan ganawar kwanaki uku da ya yi da sassa da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar.

Ma’aikatar ta shirya taron ne domin fitar da wani tsari na tsarin kiwon lafiya a Nijeriya.

A cewar Pate, ma’aikatan fannin lafiya dubu 400,000 sun haɗa da ma’aikatan kiwon lafiya na al’umma, ma’aikatan jinya, ungozoma, masu haɗa magunguna, likitoci, masana kimiyya, masu fasaha da kuma mataimaka masu aiki a tsarin kiwon lafiyar Nijeriya.

“Ba su isa ba idan kuna tunanin cewa wannan adadin zai iya kula da mutane miliyan 220. Tsarin likitanmu ga jama’a ya yi ƙasa da abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke tsammani.

“Don haka har yanzu akwai sauran damar samar da ƙari har ma a samu tara saboda a duniya, akwai ƙarancin ma’aikatan kiwon lafiya, akwai kusan ƙarancin mutane miliyan 18,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *