Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Ra’ayin ‘yan Afirka kan haɗin gwiwar Sin da Afirka ya fi muhimmanci

Daga CMG HAUSA

Game da kalaman ƙasar Amurka da suka jibanci haɗin-gwiwar ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata cewa, abun da Amurka ta fada, ba shi da muhimmanci, maimakon hakan ra’ayin ‘yan Afirka kan haɗin-gwiwarsu da ƙasar Sin shi ne mafi ma’ana.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, wanda ke ziyara a Afirka ta Kudu a jiya Litinin, ya bayyana cewa, ƙasarsa ba ta da nufin bai wa ɓangarori daban-daban zabi tsakanin Amurka da Sin, kuma abun da Amurka take fata shi ne, a samar da wani zabi na ainihi.

Har wa yau, fadar White House dake Amurka ta fitar da takardar manyan tsare-tsarenta kan yankunan dake kudu da hamadar Sahara, inda ta ce, ƙasar Sin na mayar da nahiyar Afirka a matsayin muhimmin dandali, wajen neman cimma muradun kasuwanci da siyasa, da rage alakokin Amurka da jama’a, gami da gwamnatocin ƙasashen Afirka.

Wang Wenbin ya ce, an cimma ɗimbin nasarori wajen gudanar da hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, al’amarin da ya zama sanin kowa, kana, babu wanda ya cancanta ya bata sunan haɗin-gwiwar ɓangarorin biyu.
Ya ce kasashen Afirka ba sa buƙatar aminiya wadda za ta rika jirkita gaskiya. Hanyoyin jirgin ƙasa, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa, da manyan gine-ginen da ƙasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Afirka, duk suna nan a zahiri, kuma idanun ‘yan Afirka a bude suke.

Wang ya ce, in dai da gaske Amurka tana son taimakawa nahiyar Afirka, ya dace ta ɗauki matakan zahiri, maimakon ta yi amfani da manyan tsare-tsarenta kan nahiyar Afirka, don hana ci gaban haɗin-gwiwar Afirka da sauran wasu ƙasashe.

Fassarawar Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *